Majidadin masarautar Hadejia, Alhaji Yahaya Kwatalo, ya mutu

Majidadin masarautar Hadejia, Alhaji Yahaya Kwatalo, ya mutu

Allah ya yi wa Alhaji Yahaya Kwatalo, majidadin masarautar Hadejia ta jihar Jigawa, rasuwa.

Sanaarwar mutuwar maji dadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da masarautar Hadejia ta wallafa a shafinta na tuwita.

Masarautar ba ta bayar da wani karin bayani dangane da mutuwarsa ba.

A jiya, Litinin, ne Legit.ng ta sanar da cewa Alhaji Umaru Yakubu, Dan'iyan Katagum, basarake a masarautar Azare ya mutu ranar Litinin, kamar yadda majiyar jaridar SaharaReporters ta sanar da ita.

Majiyar ta bayyana cewa ya mutu ne da safiyar ranar Litinin a Azare.

Ibrahim Hassan Hadejia, sanata mai wakiltar Jigawa ta gabas, ya ce azumi, zafin rana da karancin lafiya ne silar yawaitar mutuwar mutane a jihar Jigawa.

Rahotanni sun bayyana cewa dumbin mutane sun mutu a cikin kwana hudu a yankin karamar hukumar Hadejia, lamarin da yasa wasu ke alakanta lamarin da annobar cutar korona.

Sai dai, a wata hira da jariidar Vanguard ta yi da shi, sanatan ya ce kwamitin da aka kafa ya gano cewa mutane 46 ne suka mutu, kuma su ma babu shaidar cewar korona ce ta kashesu.

DUBA WANNAN: Rigar kowa: Ibrahim Inuwa, shugaban NSE na farko daga arewa, ya mutu

Ya kara da cewa mutanen da ke mutuwa dattijai ne da ke fama da cututtuka daban - daban, ya kara da cewa an gargadesu a kan kar su yi azumi, amma su ka yi burus da gargadin.

"Kwamitin mutum biyar, na hadin gwuiwa tsakanin hukumar lafiya ta duniya (WHO) da gwamnatin jiha, da aka kafa ya gano cewa mutane 46 ne suka mutu.

"Gwamnan jihar Jigawa ne ya kafa kwamitin bayan ya karanta labarin cewa mutane 100 sun mutu a Hadejia.

"Kwamitin ya yi tambayoyi ga iyalan mamatan domin gano abinda ya kashe yan uwansu, sannan kuma sun gwadasu. Sun gwada 'ya'yansu, matansu da makusantansu, amma ba a samu mai dauke da cutar korona ba

"Da ma akwai batun matsalar zazzabin cizon sauro a Hadejia, ga zafin rana, sannan ga jama'a suna azumi.

"Duk mutanen da ake cewa sun mutu dattijai ne da ke fama da wasu cututtukan, kuma an fada musu cewa kar su yi azumi, amma basu yi aiki da shawarar ba.

"Azumi, zafin rana, hadi da karancin koshin lafiyar da dattijan ke fama dasu, sune suka haddasa yawaitar mace-macen da suka faru," a cewar Sanatan.

Sanatan ya kara da cewa gwamnatin jihar Jigawa ta dauki matakan dakile yaduwar annobar cutar korona da sauran cutuutuka da ke barazana ga rayuwar jama'a.

Ya zuwa yanzu akwai jimillar mutane 38 da aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar korona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng