Hukumar EFCC ta kama yan China 2 da laifin baiwa shugaban EFCC cin hancin N100m

Hukumar EFCC ta kama yan China 2 da laifin baiwa shugaban EFCC cin hancin N100m

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon, EFCC, reshen jahar Sakkwato ta kama wasu mutane biyu yan kasar China da laifin yi ma shugaban ta tayin cin hanci.

EFCC ta bayyana haka ne a shafinta na Facebook a ranar Talata, inda tace Meng Wei Kun da Xu Koi sun yi ma shugaban EFCC na reshen Sakkwato tayin cin hancin naira miliyan 100.

KU KARANTA: Dan kasar China mai cutar Coronavirus ya yi asarar $300,000 a hannun EFCC

Hukumar EFCC ta kama yan China 2 da laifin baiwa shugaban EFCC cin hancin N100m
Hukumar EFCC ta kama yan China 2 da laifin baiwa shugaban EFCC cin hancin N100m Hoto: EFCC Facebook
Asali: Facebook

Da farko sun fara yi ma shugaban, Abdullahi Lawal tayin cin hancin N50,000,000 don ya dakatar da binciken da yake yi game da kamfanin China Zhonghao Nig Ltd bisa wasu ayyuka da take yi.

A tsakanin shekarar 2012 da 2019 ne gwamnatin jahar Zamfara ta baiwa kamfanin aikin naira biliyan 50 don ginin tituna a garin Gummi, Bukkuyum, Anka da Nassarawa a jahar Zamfara.

Haka zalika gwamnatin ta baiwa Chanisawan aikin gina famfon tuka tuka mai amfani da hasken rana 168 a kananan hukumomi 14 na jahar Zamfara, amma duk ta yi watsi da ayyukan.

Wannan tasa EFCC reshen Sakkwato ta shiga binciken badakalar dake tattare da aikin, inda Chanisawan suka sake tunkarar Abdullahi Lawal da N100,000,000 don ya manta da binciken.

Abin ka da kwararre, sai Lawal ya bi su yadda suke so da amincewa, har zuwa ranar Litinin, 11 ga watan Mayu inda wakilan kamfanin guda biyu Meng Wei Kun da Xu Kuoi suka same shi.

Meng Wei Kun da Xu Kuoi sun kawo masa tsabar kudi naira miliyan 50 har cikin ofishinsa dake babban ofishin hukumar EFCC a kan titin filin jirgin sama na jahar Sakkwato.

Nan da nan Lawal ya sa aka kama Meng Wei Kun da Xu Kuoi, bayan sun tabbatar masa wannan kashi na farko ne na kudin, sauran cikon naira miliyan 50 na nan tafe.

Hukumar EFCC ta kama yan China 2 da laifin baiwa shugaban EFCC cin hancin N100m
Hukumar EFCC ta kama yan China 2 da laifin baiwa shugaban EFCC cin hancin N100m Hoto: EFCC Facebook
Asali: Facebook

A wani labari kuma, Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta sanar da kwace dala dubu 300 daga hannun wani mutumi dan kasar China, Li Yan Pin.

Alkalin babbar kotun tarayya, Mai Sharia Babatunde Quadri ne ya bayar da izin kwace makudan da suka kai kimanin naira 116, 853, 003.71.

Sanarwa daga hukumar EFCC da ta samu sa hannun kakaakinta, Dele Oyewale ta bayyana cewa Alkalin ya fasa daure mutumin saboda yana dauke da alamomin cutar Coronavirus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel