Cocin katolika ta mika asibitocinta 245 ga FG don a yaki annobar korona

Cocin katolika ta mika asibitocinta 245 ga FG don a yaki annobar korona

Kungiyar limaman Cocin katolika da ke Najeria (CBCN) ta mika dukkan asibitocinsu 425 ga gwamnati domin mayar da su cibiyar killace masu cutar korona.

Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya sannan shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da annobar korona (PTF), ne ya sanar da hakan ranar Litinin yayin taro da manema labarai a Abuja.

Mustapha ya ce CBCN ta damka dukkan asibitocin ga gwamnati domin mayar da su cibiyar killace masu cutar korona.

A cikin makon jiya ne cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeria (NCDC) ta sanar da cewa babu wata jiha da take da isashen wurin duba masu cutar korona a cibiyoyinsu na killacewa.

A cewar Mustapha, gudunmawar asibitocin da CBCN ta bayar zai taimaka matuka wajen kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi a yaki da annobar korona.

"Ina mai yi wa gwamnonin jihohin Najeriya albishir din cewa Cocin katolita ta bayar da gudunmawar dukkan asibitocinta 245 da ke fadin Najeriya domin a yi amfani da su a matsayin cibiyar killacewa.

"Wannan hobbasa da Cocin ta yi zai taimakawa jihohi wajen samun karin cibiyoyin killace masu dauke da kwayar cutar korona," a cewarsa.

Cocin katolika ta mika asibitocinta 245 ga FG don a yaki annobar korona
Cocin katolika ta mika asibitocinta 245 ga FG don a yaki annobar korona
Asali: Twitter

Sannan ya cigaba da cewa, "gwamnoni zasu iya karbar asibitocin Cocin katolika da ke jihohinsu daga hannun manyan shugabannin Cocin na jiharsu."

A wani labarin na Legit.ng, kakaakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa majalisa za ta bi diddigin yadda gwamnatin Buhari za ta kashe bashin da bankin lamuni, IMF ya baiwa Najeriya.

DUBA WANNAN: Dokar kulle: Alkalan kotun tafi da gidanka sun sha da kyar a hannun fusatattun matasa a Taraba

Femi ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake ganawa da kungiyoyi masu zaman kansu, inda yace ta hakan ne zasu tabbatar an kashe kudaden bisa tsarin da aka amso su.

A watan Afrilu ne IMF ta amince da bukatar Najeriya na neman taimakon kudin gaggawa da suka dala biliyan 3.4 domin cike gibin da ta samu a kudadenta a dalilin barkewar COVID-19.

Daily Nigerian ta ruwaito kakaakin na cewa akwai kudurin dokar farfado da tattalin arziki da majalisar take aiki a kansa a yanzu, kuma da zarar ta gama zata gabatar da shi don tattaunawa.

Dokar za ta rage haraji da kashi 50 ga kamfanonin da basu sallami ma’aikatansu saboda Corona ba, duk wani batu da ya shafi yaki da COVID-19 za su dauke shi da matukar muhimmanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel