Gwamnoni zasu gudanar da taro ranar Laraba domin tattauna muhimman abubuwa 4

Gwamnoni zasu gudanar da taro ranar Laraba domin tattauna muhimman abubuwa 4

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 zasu gudanar da wani muhimmin taro ranar Laraba domin tattaunawa a kan halin da kasa ke ciki dangane da annobar korona.

Kamar yadda bayanai suka bayyana, gwamnonin zasu tattauna a kan dokar kulle da kuma tasirin tallafin rage radadi da aka rabawa 'yan kasa.

Kazalika, gwamnonin zasu tattauna a kan kudirinan na hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) da majalisa ke son zartarwa da kuma tsarin tabbatar da farfadowar tattalin arzikin kasa.

Kakakin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Abdulrazaque Bello Barkindo, ya ce wannan shine karo na takwas da gwamnonin zasu gudanar da taro ta yanar gizo tun bayan barkewar annobar cutar korona.

Ya bayyana cewa gwamnonin na gudanar da taron ne domin tattaunawa tare da samar da mafita ga jama'a da kasa a kan annobar korona da ta shafi kowanne bangare na kasa.

Barkindo ya ce, taron, wanda za a fara da misalin karfe 2:00 na ranar Laraba, zai karbi rahoto daga jihohi a kan yadda rabon tallafin rage radadi ya kasance a jihohinsu.

Gwamnoni zasu gudanar da taro ranar Laraba domin tattauna muhimman abubuwa 4

Gwamnoni zasu gudanar da taro ranar Laraba domin tattauna muhimman abubuwa 4
Source: Facebook

Jawabin ya kara da cewa, za a gayyaci shugaban kamfanin dillancin man fetur na kasa, Mista Mele Kyari, domin ya bayar da bayani a kan tallafi da gudunmawar da NNPC ta bayar tun bayan barkewar annobar korona.

DUBA WANNAN: Jami'an tsaro sun kashe 'yan Najeriya 11 bayan tsawaita dokar kulle - NHRC

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, wani alkali a kotun kasar Amurka ya amince da bukatar gwamnatin Najeriya na gudanar da binciken kwakwaf a kan asusun wasu tsofin manyan kusoshin gwamnatin Najeriya, kamar yadda jaridar 'TheCable' ta rawaito.

A watan Satumba na shekarar 2019 ne wata kotun kasar Ingila ta zartar da hukuncin cin tarar Najeriya $9.6bn saboda saba yarjejeniyar kwangilar da ta kulla da wani kamfani mai suna P&ID.

Domin kalubalantar wannan hukunci, gwamnatin Najeriya ta shigar da kara a gaban wata kotun kasar Amurka, inda ta nemi izinin gudanar da bincike a kan asusun wasu manyan kusoshin gwamnatin da ta gabata.

KARANTA CIKAKKEN LABARIN A NAN: Amurka ta amince da bukatar Najeriya na binciken asusun bankin Jonathan, Diezani, Lukman da sauransu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel