Wata matashiya ta yi wa mahaifinta wanda ke sauke Qur’ani a kwana 3 addu’a

Wata matashiya ta yi wa mahaifinta wanda ke sauke Qur’ani a kwana 3 addu’a

- Wata budurwa 'yar Najeriya ta bayyana mahaifinta mai shekaru 96 a kafafen sada zumuntar zamani

- Alim Joda ta ce mahaifin ta yana sauke Qur'ani duk bayan kwanaki uku sannan yana limamci duk da tarin shekarunsa

- Budurwar ta yi addu'a albarka ga mahaifin nata tare da kyakyawan karshe

Wata matashiyar budurwa mai suna Alim Joda ta wallafa labarin mahaifinta a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Alim Joda ta ce duk da mahaifinta na da shekaru 96 a duniya, yana sauke Qur'ani sau daya a duk bayan kwana uku sannan yana iya azumin watan Ramadan. Ba a nan ya tsaya ba, yana limancin sallar taraweehi a kowacce rana.

Sau da yawa ana kallon tsofaffi a matsayin mutane masu rauni kuma basu iya yi wasu ayyuka saboda shekarunsu.

Amma kuma, akwai wadanda ko bayan shekarunsu sun yi nisa ba sa samun rashin kuzarin.

A addinin Musulunci, ba a wajabta wa tsofaffai azumi ba ko kuma marasa lafiya.

Mahaifin Alim Joda mai shekaru 96 kuwa ya bayyana cewa ba azumi kadai zai iya jurewa ba.

Alim Joda ta wallafa hotunan mahaifinta a tsaye yayin da yake limanci ba tare da gajiyawa ba.

Ta ce: "Wannan ne mahaifina mai suna Hajj HammanJoda Fari. Yana sauke Qur'ani a cikin kwanaki uku. Shekarunsa 96 kuma yana limancin sallar taraweeh.

"Ya Allah ka saukake wa iyayenmu kuma ka albarkacesu da karshe mai kyau. Allah ka ji kan su kamar yadda suka ji kanmu muna kanana."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya aika sunayen jakadu 42 majalisa domin tabbatar da su

A wani labari na daban, jami'an 'yan sanda sun ceto wasu mata biyu da ake zargin 'yan bindiga ne suka sace su a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Ya yi bayanin cewa sun yi nasarar ceto matan bayan kiran da suka samu a ranar Alhamis din makon da ya gabata.

'Yan bindigan da za su kai 10 sun tsinkayi kauyen Sabon Layi a babura dauke da bindigogi kirar AK 47 inda suka yi awon gaba da matan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel