P&ID: Amurka ta amince da bukatar Najeriya na duba asusun bankin Jonathan da Diezani

P&ID: Amurka ta amince da bukatar Najeriya na duba asusun bankin Jonathan da Diezani

- Wata kotun kasar Amurka ta amince da bukatar gwamnatin Najeriya da biciken asusun tsohon shugaba kasa, Gooluck Jonathan

- Kazalika, kotun ta amince a binciki asusun bankin uwargidan Jonathan, Dame Patience, da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison-Madueke

- Ministan shari na kasa, Abubakar Malami, ya ce akwai kwararan hujjoji da ke nuna an hada baki da wasu manyan kusoshin gwamnatin baya domin damfarar Najeriya

Wani alkali a kotun kasar Amurka ya amince da bukatar gwamnatin Najeriya na gudanar da binciken kwakwaf a kan asusun wasu tsofin manyan kusoshin gwamnatin Najeriya, kamar yadda jaridar 'TheCable' ta rawaito.

A watan Satumba na shekarar 2019 ne wata kotun kasar Ingila ta zartar da hukuncin cin tarar Najeriya $9.6bn saboda saba yarjejeniyar kwangilar da ta kulla da wani kamfani mai suna P&ID.

Domin kalubalantar wannan hukunci, gwamnatin Najeriya ta shigar da kara a gaban wata kotun kasar Amurka, inda ta nemi izinin gudanar da bincike a kan asusun wasu manyan kusoshin gwamnatin da ta gabata.

Daga cikin wadanda gwamnatin tarayya ta nemi izinin binciken asusunsu da hada-hadar kudin da ta gudana a asusunsu sun hada da; tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, uwargidansa; Dame Patience, tsohuwar ministar man fetur; Diezani Allison-Madueke da Rilwanu Lukman.

A cewar Abubakar Malami, ministan shari'a na kasa, "akwai dalilai masu karfi da ke nuna cewa akwai hannun ministoci da manyan kusoshin gwamnati a yunkurin damfarar Najeriya makudan kudade."

Amurka ta amince da bukatar Najeriya na duba asusun bankin Jonathan da Diezani

Jonathan da Dame Patience
Source: Instagram

Malami Ya ce tun asali kamfanin P&ID bashi da niyyar kaddamar da kwangilar da aka kulla yarjejeniyarta.

DUBA WANNAN: Jami'an tsaro sun kashe 'yan Najeriya 11 bayan tsawaita dokar kulle - NHRC

Ministan ya ce kamfanin ya bawa wasu manyan jami'an gwamnati cin hanci domin su kawar da kansu daga rashin iko da karfin da ya ke da shi na gudanar da kwangilar da ko allura ba a ajiye da sunan fara kaddamar da ita ba.

Da ya ke zartar da hukunci ranar Alhamis, alkalin kotun, Lorna Schofield, ya ce bukatar gwamnatin Najeriya ta cimma dukkan bukatun da shari'a ke bukata.

Amma, kotun ta ki amincewa da bukatar gwamnatin Najeriya na boyewa kamfanin P&ID sakamakon bincikenta.

Alkalin kotun ya ce dole gwamnatin Najeriya ta bawa kamfanin P&ID damar duba duk takardun da ta bankado yayin binciken da zata gudanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel