Yadda 'yan sanda suka kubutar da mata biyu daga masu garkuwa da mutane

Yadda 'yan sanda suka kubutar da mata biyu daga masu garkuwa da mutane

Jami'an 'yan sanda sun ceto wasu mata biyu da ake zargin 'yan bindiga ne suka sace su a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Ya yi bayanin cewa sun yi nasarar ceto matan bayan kiran da suka samu a ranar Alhamis din makon da ya gabata.

'Yan bindigan da za su kai 10 sun tsinkayi kauyen Sabon Layi a babura dauke da bindigogi kirar AK 47 inda suka yi awon gaba da matan.

"Daga nan ne DPO na karamar hukumar Kurfi ya jagoranci rundunar Operation Puff Adder da 'yan sa kai inda suka bi 'yan bindigar har kauyen Kaguwa sannan suka yi musayar wuta," takardar tace.

Kamar yadda Isah ya bayyana, rundunar ta yi nasarar ceto Huraira Murnai mai shekaru 60 da Hadiza Murnai mai shekaru 50.

Yadda 'yan sanda suka kubutar da mata biyu daga masu garkuwa da mutane

Yadda 'yan sanda suka kubutar da mata biyu daga masu garkuwa da mutane. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Jerin jihohi 6 da WHO za ta gwada maganin korona a Najeriya

Ya ce 'yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji amma 'yan sanda sun fara bincike a kan harin da aka kai wa kauyen.

A wani labari na daban, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya bayyana cewa wata kungiyar 'yan bindigar sun tsare babban titin kauyen Dankar da ke karamar hukumar Batsari ta jihar inda suka dinga yi wa 'yan kauyen fashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel