Garin dadi: ATM na rabawa mutane shinkafa a lokacin da ake tsaka da annobar COVID-19

Garin dadi: ATM na rabawa mutane shinkafa a lokacin da ake tsaka da annobar COVID-19

- Masu bukatar shinkafa a kasar Indonesiya a yanzu suna iya zuwa wajen na’urar ATM mai zubo da shi

- Gwamnatin Indonesiya ta samar da “ATM din shinkafa” domin jama’ar kasar

- Wadanda suka dogara a fita kullun kafin samun hasafi, marasa aiki, da wadanda basu mallaki gida ba da talakawa ne ke cin moriyar shirin

Gwamnatin Indonesiya ta tanadi na’urar ATM mai zubo da shinkafa a kokarinta na tabbatar da talaka ya samu abinci yayinda kasar ke gwagwarmaya da annobar COVID-19.

Annobar ta jefa miliyoyin yan kasar Indonesiya a cikin wani hali na gwagwarmayar rayuwa, CNA ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa wata uwa mai shekaru 28 wacce aka ambata da Syafri na daga cikin tarin mutanen da suka bi layi a sansanin soji a Depok, da ke wajen Jakarta, domin karban shinkafar wanda yawansa bai wuci 1.5kg ba.

Ta ce: “Kamfanin da nake aiki ta sallame ni a makon da ya gabata sannan shima mijina an sallame shi ba tare da albashin sallama ba. Koda dai tallafin shinkafan ba mai yawa bane, yana taimakawa sosai a wannan yanayi da ake ciki."

Wadanda ke cin moriyar tallafin sun hada da wadanda suka dogara a fita kullun kafin samun hasafi, marasa aiki, da wadanda basu mallaki gida ba da talakawa.

Garin dadi: ATM na rabawa mutane shinkafa a lokacin da ake tsaka da annobar COVID-19

Garin dadi: ATM na rabawa mutane shinkafa a lokacin da ake tsaka da annobar COVID-19 Hoto: CNA
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Wata tsohuwar yar majalisa ta kamu da korona a jihar Benue, ta kuma ziyarci gidan gwamnati

Na’urar shinkafan ya yi kama da na kudi da aka sani, sai dai wannan na dauke da ma’aunin nauyin shinkafa wanda ake zubowa mabukata da shi.

Garin dadi: ATM na rabawa mutane shinkafa a lokacin da ake tsaka da annobar COVID-19

Garin dadi: ATM na rabawa mutane shinkafa a lokacin da ake tsaka da annobar COVID-19 Hoto: CNA
Source: UGC

A wani labarin kuma, kakaakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa majalisa za ta bi diddigin yadda gwamnatin Buhari za ta kashe bashin da bankin lamuni, IMF ta baiwa Najeriya.

Femi ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake ganawa da kungiyoyi masu zaman kansu, inda yace da haka ne zasu tabbata an kashe kudaden bisa tsarin da aka amso su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel