Wata tsohuwar yar majalisa ta kamu da korona a jihar Benue, ta kuma ziyarci gidan gwamnati

Wata tsohuwar yar majalisa ta kamu da korona a jihar Benue, ta kuma ziyarci gidan gwamnati

Gwamnatin jihar Benue, a ranar Litinin, ta tabbatar da samun mutum na uku da ta kamu da cutar COVID-19 a jihar. Ta kasance 'yar majalisar wakilai a jumhuriya ta uku kuma tsohuwar kwamishina a jihar.

Gwamna Samuel Ortom, wanda ya yi sanarwar a yayinda ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Makurdi, ya ce wacce ta kamun ta kasance Misis Rebecca Apedzan, sannan cewa ta ziyarci gidan gwamnatin a ranar Lahadi.

Gwamna Ortom, ya shawarci duk wadanda suka yi hulda da ita a yan kwanakin da suka gabata da su je su duba lafiyarsu.

Wata tsohuwar yar majalisa ta kamu da korona a jihar Benue, ta kuma ziyarci gidan gwamnati

Wata tsohuwar yar majalisa ta kamu da korona a jihar Benue, ta kuma ziyarci gidan gwamnati Hoto: Channels TV
Source: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa an sanar da kamuwar mutum na ukun ne kwanaki bakwai bayan samun mai dauke da cutar na biyu a jihar.

Tsawon wata guda kenan da jihar ta samu mutum na farko da ke da cutar, wacce ta kasance wata mace da ta dawo daga kasar Ingila a ranar 28 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Kaduna ta samu miliyan N1.9 daga hannun wadanda suka karya dokar kulle cikin kwanaki 2

A wani labarin kuma, mun ji cewa 'Yan sanda a jihar Kano a ranar Litinin sun rufe dukkan kofofin shiga Kasuwar Kwari da ke Kano domin cigaba da tabbatar da dokar kulle da Shugaba Muhammadu Buhari ya saka a jihar domin dakile yaduwar korona.

Wa'adin kullen na sati biyu zai kare ne a jiya Litinin 11 ga watan Mayu dai kuma Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kuma tsawaita dokar kulle da sati daya.

Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a jihar sun kai 666 a ranar Litinin 11 ga watan Mayun shekarar 2020.

Jami'an tsaro a ranar Alhamis da ta gabata sun hana yan kasuwa da kwastomominsu shiga kasuwar a yayin da gwamnatin jihar ta sassauta dokar kullen a kwanaki biyu cikin kowace mako.

Gwamna Abdullahi Ganduje a makonni biyu da suka shude ya sanar da kasuwannin Yan Kaba da Yan Lemo ne kawai aka bawa damar budewa a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel