Ogun: Shugabanin Jam’iyyar PDP su na rigima da Yaran Buruji Kashumu

Ogun: Shugabanin Jam’iyyar PDP su na rigima da Yaran Buruji Kashumu

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa rigima ta cabe a cikin jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ogun a kan sha’anin shugabanci bayan na-hannun daman Buruji Kashumu sun karbe jam’iyya.

Jaridar ta ce akwai alamun cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP na jihar Ogun za su sheka kotu a sakamakon kaddamar da yaran Buruji Kashumu da aka yi a matsayin shugabannin jihar.

Idan ba za ku manta ba a 2016 ne bangaren Buruji Kashumu su ka gudanar da zabe, su ka fito da shugabanni a karkashin Bayo Dayo, kuma har su ka yi galaba a kan ‘yan jam’iyyar a kotu.

A halin yanzu wa’adin shugaba Bayo Dayo da ‘yan majalisarsa ya cika. Sai dai kuma uwar jam’iyya ta nuna cewa ba ta tare da yaran Kashamu da su ke cigaba da rike mata jam'iyyar.

Uwar jam’iyyar ta PDP ta na tare ne da bangaren Ladi Adebutu a jihar Ogun. Wannan lamari ya sake jagwalgwala alakar bangarensu Kashamu da kuma shugaba na kasa Uche Secondus.

KU KARANTA: Kusoshin PDP sun hara harin kujerar Shugaban Jam'iyya a Kaduna

A wani jawabi da shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus da sakatarensa, Umaru Tsauri, su ka fitar, sun yi fatali da zaben shugabannin da su sanata Buruji Kashamu su ka shirya.

“Nauyin shirya zaben shugabanni a kowane matakin jam’iyya ya rataya ne a kan majalisar NEC/NWC kadai. Babu wasu shugabannin jiha da za su iya yin zabe, sai in an ba su dama.”

Abin da wannan jawabi na uwar jam’iyyar PDP ya ke nufi shi ne ba a gudanar da zaben shugabannin mazabu da na kananan hukumomi da kuma shugabannin da za su rike jihar ba.

Amma tuni sabon shugaban da ‘yan taware su ka nada, Samson Bamgbose ya maidawa NWC martani, ya ce an bi duk wasu dokokin da aka tanada wajen zabensa da ‘yan majalisarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel