Kasuwar canji: Dala ta fara wahala a Gari, ana saida $1 a kan N445 - BDC

Kasuwar canji: Dala ta fara wahala a Gari, ana saida $1 a kan N445 - BDC

- Dala ta yi wuya a halin yanzu saboda takunkumin zirga-zirga da aka maka

- An saida Dalar Amurka a kan N445 a jiya inji shugaban ‘yan kasuwar canji

An wayi gari a farkon makon nan ana fama da matukar rashin kudin kasar waje a kasuwar canjin Najeriya. Jaridar The Punch ta kasar nan ta fitar da wannan rahoto jiya.

A jiya ranar Litinin, 11 ga watan Mayu, 2020, an saida kowace Dalar Amurka a kan N445 a kasuwar canji a sanadiyyar wahalar da Dala ta yi a cikin ‘yan kwanakin nan.

Rahotanni sun ce takunkumin zaman gidan da gwamnatin tarayya ta maka domin yaki da COVID-19 ya taimaka wajen kara kawo wahalar samun kudin kasashen ketare.

A dalilin wannan takunkumi da aka sa, jiragen sama ba su sauka kuma ba su iya tashi a Najeriya. Wannan ya sa Dalar Amurkan ta fara wahala sosai a wasu wurare a cikin kasar.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar canji na Najeriya, Alhaji Aminu Gwadabe ya ce hana jirage tashi a wannan marra ne ya jawo Naira ta kife a kan Dala, har ta doshi akalla N425.

KU KARANTA: Naira ta yi raga-raga, Dala ta koma N420 a kasuwar canji

Kasuwar canji: Dala ta fara wahala a Gari, ana saida $1 a kan N445 - BDC
Gwamnan CBN Godwin Emefiele a wajen wani taro a Najeriya
Asali: Twitter

Aminu Gwadabe ya shaidawa ‘yan jarida cewa ana cinikin Dala ne yanzu a kan N425 zuwa N445 a kasuwannin canji. Ya ce CBN ta yi alkawarin kawowa kasuwar agaji.

Ya ce: “Duk da haka, alkawarin da gwamnan babban bankin CBN ya yi wa masu zuba hannun jari a Najeriya ya taimaka wajen rike farashin a kan N445 har zuwa jiya.”

Gwadabe ya bayyana cewa yunkurin da gwamnan CBN ya ke yi ne ya hana Dalar Amurkar tashi fiye da N445. Har zuwa jiya da yamma dai Dalar ba ta haura N445 ba.

‘Yan kasuwa sun fara rokon gwamnan CBN ya saidawa bankuna Dala domin masu bukata. Labari ya fara zuwa mana cewa Dalolin sun fara isa hannun wasu bankuna jiya.

Manyan bankunan cikin gida sun dawo da saidawa masu neman biyan kudin makaranta Dala a cikin makon nan. Haka zalika ana bada Dalar ga kananan ‘yan kasuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel