Buhari ya nada Mohammad Shehu a matsayin sakataren RMAFC
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Mohammed Bello Shehu, a matsayin sakataren hukumar kasafin kudaden haraji da gwamnatin tarayya ta samu.
Shehu, wanda nadinsa ya fara aiki a ranar 19 ga watan Maris, zai shafe zangon farko mai wa'adin shekaru biyar a hukumar RMAFC tare da zabin sabunta nadinsa a zango na biyu idan shugaban kasa ya ga dama.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Willie Bassey, darektan yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayya. Sanarwar ta fito ne da yammacin ranar Litinin.
A cewar sanarwar, shugaba Buhari ya sake amincewa da nadin Bitrus Danharbi Chinoko a matsayin babban darektan CMD (Centre for Management Development) Lagos.
Nadinsa zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Afrilu.

Asali: Twitter
Kafin nadinsa a matsayin babban darekta mai cikakken iko, Mista Chinoko ya kasance mukaddashin babban darektan CMD.
DUBA WANNAN: Jami'an tsaro sun kashe 'yan Najeriya 11 bayan tsawaita dokar kulle - NHRC
"Shugaba Buhari ya tayasu murna tare da bukatar su yi amfani da kwarewarsu domin kawo sauye - sauye masu amfani da muhimmanci a hukumomin da zasu jagoranta," a cewar sanarwar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng