Basaraken jihar Bauchi, Alhaji Umaru Yakubu, ya mutu

Basaraken jihar Bauchi, Alhaji Umaru Yakubu, ya mutu

Alhaji Umaru Yakubu, Dan'iyan Katagum, basarake a masarautar Azare ya mutu ranar Litinin, kamar yadda majiyar jaridar SaharaReporters ta sanar da ita.

Majiyar ta bayyana cewa ya mutu ne da safiyar ranar Litinin a Azare.

Rahotannin na yawan kawo labarin yawaitar mace - macen jama'a a garin Azare a cikin 'yan kwanakin baya bayan nan.

Yawaitar mace - macen jama'ar ya na cigaba da saka tsoro, fargaba da zaman zulumi a tsakanin mazauna garin Azare.

Ibrahim Baba, tsohon mamba mai wakiltar mazabar Azare a majalisar wakilai, ya rubutawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wasika.

A cikin wasikar, tsohon dan majalisar ya yi zargin cewa an samu barkewar annobar cutar korona a garin Azare.

Tsohon dan majalisar ya yi zargin cewa annobar korona ta hallaka fiye da mutane 100 a cikin sati daya a garin Azarae.

Kazalika, a ranar Alhamis da ta gabata, wani tsohon dan takara a jam'iyyar PDP daga Azare, Musa Azare, ya rubuta wasika zuwa ga gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.

Basaraken jihar Bauchi, Alhaji Umaru Yakubu, ya mutu
Marigayi Dan'iyan Katagum, Alhaji Umaru Yakubu
Asali: Facebook

A cikin wasikar, Musa ya yi zargin cewa akwai sabbin kaburbura fiye da 300 da aka haka a makabartar garin Azare.

Ya kara da cewa, babban abin damuwar shine yadda jama'a ke daukan gawarwaki zuwa makabarta ba tare da yin biyayya ga matakan hukuma a kan kare kai da dakile yaduwar kwayar cutar korona ba.

DUBA WANNAN: Jami'an tsaro sun kashe 'yan Najeriya 11 bayan tsawaita dokar kulle - NHRC

"Yawancin mutanen da ke mutuwa dattijai ne da shekarunsu suka zarce 60. Tun bayan mutuwar Fatima Adamu, mahaifiyar ministan ilimi, Adamu Adamu, ake samun yawaitar mutuwar mutane.

"Ya zuwa yanzu, mutanen da suka mutu a Azare sun zarce 300. Babu wani bincike da aka gudanar domin danin musabbabin mutuwarsu," a cewar Musa.

Musa ya bukaci gwamnati ta samar da cibiyar gwajin kwayar cutar korona a garin Azare don sanin ko annobar ce kashe jama'a.

Sai dai, gwamnatin jihar Bauchi ta musanta cewa akwai alaka tsakanin yawaitar mace - macen jama'a a garin Azare da kuma barkewar annobar cutar korona.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce tsananin zafi ne ke haddasa yawaitar mace - macen dattijai marasa koshin lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel