Tambuwal: Gwamnatin Sokoto za ta biya Malaman sa-kai da ke aikin jinyar COVID-19
- Gwamnan Sokoto ya dauki Malaman lafiyan sa-kai aikin lura da masu COVID-19
- A kowace rana Gwamnatin Tambuwal za ta rika biyan masu aikin kudin alawus
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya bada sanarwar bada alawus na N15, 000 a kowace rana ga wadanda su ka zabi su yi aikin jinyar masu dauke da cutar COVID-19.
Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi alkawarin biyan wannan kudi ga malaman lafiyan da za su yi aiki a dakunan da ake killace wadanda su ka kamu da Coronavirus a jihar Sokoto.
Kwamishinan lafiya wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da ke yaki da annobar COVID-19 a Sokoto, Ali Inname ya ce malaman lafiya fiye da 10, 000 su ka bukaci su yi wannan aiki.
Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da mutane 1,000 na farko da aka zaba domin su yi aikin. Mai girma gwamna Aminu Tambuwal ya ce wasu za su yi aiki daga wajen dakunan jinyar.
KU KARANTA: Wasu Gwamnonin sun sa siyasa a lamarin Coronavirus - Ganduje
Za a biya N12500 ga kowane daga cikin ma’aikatan jinyan da su ke aiki daga wajen dakunan killace marasa lafiyan. Sauran malaman asibiti za su samu karin 50% a alawus dinsu.
Ma’aikatan lafiyan da aka tura yankunan da ke kan iyaka a jihar za su samu karin 25% a na su alawus din a kowace rana. Likitoci da ungonzoma da leburori ne za su amfana da karin.
Da ya ke jawabi, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi alkawari cewa gwamnatinsa za ta samar da isassun kayan kayan aiki da na kare lafiya da malaman asibiti za su rika aiki da su.
Aminu Waziri Tambuwal ya ce za a rikidar da wasu otel da ke hannun gwamnatin jihar Sokoto su zama wurin killace masu cutar COVID-19. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.
Gwamnatin ta ce daga cikin wadanda aka fara dauka aikin akwai ungunzoma 106, malaman dakin bincike 30, masu bada kayan magani 15, likitoci 44 da wasu ma’aikatan na dabam.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng