Hargitsi ya barke a garin Abuja bayan jami’in dan sanya ya harbe wani mutum

Hargitsi ya barke a garin Abuja bayan jami’in dan sanya ya harbe wani mutum

Tashin hankali da rudani ya barke a Karmo a ranar Litinin sakamakon kashe wani mutum da dan sanda ya yi.

Lamarin ya faru a babban birnin tarayya ne da yammacin Lahadi. Wanda aka kashe sunansa Solomon Eze, babban dan kasuwa.

Har yanzu dai babu takamaiman dalilin da yasa dan sandan ya kashe mutumin. Masu zanga-zangar sun yi barazanar kurmushe ofishin 'yan sandan sakamakon harbin.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, Anjuguri Manzah, ya ce an gano dan sandan a halin yanzu kuma an damke shi.

Manzah ya ce hukumar za ta yi adalci a yayin bincike don gano abinda ya kawo aukuwar lamarin, jaridar The Cable ta ruwaito.

Hargitsi ya barke a garin Abuja bayan jami’in dan sanya ya harbe wani mutum

Hargitsi ya barke a garin Abuja bayan jami’in dan sanya ya harbe wani mutum Hoto: The Cable
Source: UGC

"Dan sandan da ya harba mutumin tuni aka damke shi kuma an kama shi," kakakin ya sanar a takardar da ya fitar.

"A yayin jaje ga iyalai da abokan mamacin, kwamishinan 'yan sandan FCT yana tabbatar wa da jama'a cewa za ta tabbatar da adalci a yayin bincike tare da bayyana wa jama'a," yace.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: An kwantar da wani dan majalisar jihar Nasarawa a asibiti

A wani labarin kuma, mun ji wa akalla mutane biyar ne suka mutu sakamakon wata sabuwar rikici da ta barke tsakanin kabilun Fulani da Tibabe a jahar Nassarawa.

Daily Trust ta ruwaito baya ga kisan kai da aka yi, mutane da dama sun jikkata a rikicin daya barke a lardin Kadarko, cikin karamar hukumar Keana, a kan iyakar Nassarawa da Benuwe.

Wani dan kabilar ya bayyana cewa rikicin ya faro ne bayan wani dan Fulani ya gamu da wata mata yar tibi a gona, inda ya mata dukan kawo wuka haka nan ba tare da wani laifi ba.

Ihun da matar ta yi na neman agaji ya sa wani dan tibi dake noma a gonarsa ya yi kokarin kai mata dauki, amma bafulatanin ya fi karfinsa, kuma ya sassare shi a kai da hannu.

Amma wani jami’in kungiyar Miyetti Allah da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa matasan kabilar Tibi sun kashe musu Fulani guda uku kwanaki uku da suka wuce a Yelwata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel