COVID-19: An kwantar da wani dan majalisar jihar Nasarawa a asibiti

COVID-19: An kwantar da wani dan majalisar jihar Nasarawa a asibiti

- An mika wani dan majalisar jihar Nasarawa asibiti kan zargin da aka yi yana dauke da cutar COVID-19

- Hakan na zuwa ne makonni biyu bayan rasuwar dan majalisar jihar Nasarawa, Sulaiman Adamu, sakamakon annobar Coronavirus

- An tattaro cewa dan majalisar wanda aka sakaya sunansa, na kwance a asibitin kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafia

Makonni biyu bayan rasuwar dan majalisar jihar Nasarawa, Sulaiman Adamu, sakamakon annobar Coronavirus, an mika wani dan majalisar asibiti.

An gaggauta mika dan majalisar asibiti a jihar sakamakon zargin da aka yi yana dauke da cutar coronavirus.

Daily Nigerian ta gano cewa dan majalisar wanda aka sakaya sunansa, na kwance a asibitin kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafia.

An kwantar da dan majalisar ne a asibitin da ke babban birnin jihar a sa'o'in farko na ranar Litinin 11 ga watan Mayun 2020.

COVID-19: An kwantar da wani dan majalisar jihar Nasarawa a asibiti

COVID-19: An kwantar da wani dan majalisar jihar Nasarawa a asibiti Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

An gano cewa, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Nasarawa ta yamma yana daga cikin wadanda suka halarci jana'izar marigayin dan majalisar da korona ta halaka a makonni biyu da suka gabata.

Duk da gwamnatin jihar bata fitar da takarda dangane da hakan ba, majiya mai karfi ta tabbatar da cewa an killace dan majalisar ko a asibitin.

KU KARANTA KUMA: Yawan mace-mace a Yobe – Shugaban majalisar dattawa ya nuna damuwa kan abunda ke wakana a mahaifarsa

A baya mun ji cewa wamnatin jihar Nasarawa ta rufe majalisar dokokin jihar Nasarawa tare da bulbula feshin magani bayan mutuwar mamba, Honarabul Suleiman Adamu, sakamakon kamuwa da kwayar cutar covid-19.

Cutar coronavirus ta kashe dan majalisar jihar Nasarawa, Adamu Sulaiman, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Sulaiman ne majinyaci na farko da ya rasu sakamakon cutar covid-19 a Nasarawa tun bayan da aka gano annobar ta shiga jihar.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da mutuwar dan majalisar a yayin da yake jawabi ga manema labarai a garin Lafia, babban birnin jiha.

A yayin sanar da inda aka kwana a kan annobar cutar a jihar, Gwamna Sule ya sanar da cewa Sulaiman ya rasu tun kafin sakamakon gwajinsa ya fito.

Ya yi bayanin cewa, bayan an samu sakamakon gwajin dan majalisar, iyalansa da wadanda ke rayuwa tare dashi duk an killacesu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel