Bakuwar cuta: An birne mutum 68 a Potiskum cikin kwanaki uku

Bakuwar cuta: An birne mutum 68 a Potiskum cikin kwanaki uku

Guguwar mace-mace na ci gaba da kada wa a wasu jihohin arewa har ta kai ga jihar Yobe.

A birnin kasuwanci na Potiskum, a kalla mutum 68 ne aka birne a cikin kwanaki uku.

Suna zargin mace-macen na da alaka da cutar coronavirus.

Kwamishinan lafiya na jihar Yobe, Mohammed Lawan Gana, wanda shine mataimakin shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus ta jihar, ya ce gwamnati na binciken silar mace-macen.

Kamar yadda yace, ba za a danganta mace-macen kai tsaye da annobar Coronavirus ba kuma ba za a ce ba cutar bace ke kawo mace-macen ba.

Bakuwar cuta: An binne mutum 68 a Potiskum cikin kwanaki uku

Bakuwar cuta: An binne mutum 68 a Potiskum cikin kwanaki uku Hoto: The Nation
Source: UGC

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, ya kara da cewa gwamnati ta tura kwararru a fannin lafiya don bincikar abinda ke kawo mace-macen.

Kwamishinan yace: "Wadannan rade-radin suna faruwa. Mutane na mutuwa sakamakon cutuka da dama. Ba za mu iya cewa ba korona bace. Idan irin wannan abu na faruwa, ba a kai wa ga matsaya har sai an yi bincike.

KU KARANTA KUMA: Yawan mace-mace a Yobe – Shugaban majalisar dattawa ya nuna damuwa kan abunda ke wakana a mahaifarsa

"Amma saboda haka, mun tura kwararru a fannin lafiya. Muna so jama'a su bada hadin kai kuma kada su ji tsoro."

Amma wani mai tsaron makabarta a Potiskum wanda ya zanta da wakilin The Nation, ya ce: "Bamu san me ke kashe jama'a ba haka. Mu kanmu muna son sanin amma har yanzu bamu gane ba. Muna bukatar gwamnati da ta saka hannu don gano hakan.

"Amma kuma 'yan jarida ne kadai ke kiranmu don tambayarmu abinda ke faruwa."

Kamar yadda yace, mutane na ci gaba da mutuwa kuma makabartu na cika. Ya ce gawawwaki 68 aka birne a cikin kwanaki uku da suka gabata.

Ya ce makabartar Mamman Ali da ke kan titin Gashua ta karba gawawwaki 48 don birnewa a kwanaki uku da suka gabata.

Mai tsaron makabartar ya lissafo wasu daga cikin makabartun da ke korafin. Sun hada da na Nepay, Garin Jaji, Gishua Dabua da Bakin asibiti.

A ranar Lahadi ne shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya jinjinawa gwamnatin jihar Yobe a kan umarnin da ta bada na bincikar abinda ke kawo mace-macen a wasu sassan jihar.

Lawan ya nuna damuwarsa a kan rahoton mace-macen jama'a a Gashua, Nguru da Potiskum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel