Yawan mace-mace a Yobe – Shugaban majalisar dattawa ya nuna damuwa kan abunda ke wakana a mahaifarsa

Yawan mace-mace a Yobe – Shugaban majalisar dattawa ya nuna damuwa kan abunda ke wakana a mahaifarsa

A jiya Lahadi ne shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya nuna damuwarsa a kan yawan mace-macen da ke faruwa a jihar Yobe.

A wata takarda da mai magana da yawun Lawan, Ola Awoniyi ya fitar, ya yi kira ga yankunan da su bai wa hukumomi a jihar hadin kai don binciko abinda ke kawo mace-macen.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, Lawan ya ce, "Kokarin da gwamnati ke yi a yanzu shine bincike a kan mace-macen. Mutuwar kamar kowacce iri ce ko kuma akwai cutar da ke kawo ta. Ta hakan ne kadai za a iya shawo kan matsalar.

Yawan mace-mace a Yobe – Shugaban majalisar dattawa ya nuna damuwa kan abunda ke wakana a mahaifarsa
Yawan mace-mace a Yobe – Shugaban majalisar dattawa ya nuna damuwa kan abunda ke wakana a mahaifarsa Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Twitter

"Dole ne tallafin gwamnatin jihar a yanzu don samun sakamakon da ya dace. Yankunan ake bukata su bada hadin kai don bai wa hukumomi damar nasarar bincike."

Ya jajanta da iyalai da abokan arzikin mamatan tare da musu fatan rahama.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: El-Rufai ya sanar da mutuwar wani babban mutum a jihar Kaduna

Ya yi kira ga jama'ar yankin da su kwantar da hankalinsu kuma kada su tsorata a kan lamarin. Su jira sakamako daga hukumomin jihar don bankado silar mutuwar tare da shawo kan ta.

A wani labarin na daban, gwamnatin jihar Bauchi ta yi bayani a kan rahoton mace-macen da ke faruwa a yankin Azare na jihar.

A cewarta, yanayin zafin gari ne ke kawo mace-macen ba annobar Coronavirus ba.

Mataimakin Gwamnan jihar, Baba Tela ya sanar da manema labarai a ranar Lahadi cewa tuni aka yi bincike kuma an gano zuzuta yawan mace-macen ake yi.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya bayyana, mataimakin Gwamnan wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar, ya ce kafafen sada zumuntar zamani na ruwaito cewa mutum 300 ne suka rasu a mako daya.

Har ila yau ya jadadda cewa wannan batu ba gaskiya bane sannan kuma ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da zancen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel