Gwamnatin Bauchi ta bayyana abinda ke kawo mace-mace a jihar

Gwamnatin Bauchi ta bayyana abinda ke kawo mace-mace a jihar

Gwamnatin jihar Bauchi ta yi bayani a kan rahoton mace-macen da ke faruwa a yankin Azare na jihar.

A cewarta, yanayin zafin gari ne ke kawo mace-macen ba annobar Coronavirus ba.

Mataimakin Gwamnan jihar, Baba Tela ya sanar da manema labarai a ranar Lahadi cewa tuni aka yi bincike kuma an gano zuzuta yawan mace-macen ake yi.

Gaskiya ta yi halinta: Gwamnatin Bauchi ta bayyana abinda ke kawo mace-mace a jihar
Gaskiya ta yi halinta: Gwamnatin Bauchi ta bayyana abinda ke kawo mace-mace a jihar Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

"A kan zancen mace-macen da ke faruwa a Azare, mun samu rahotanni masu tarin yawa. Wasu sun ce mutum biyar ne, wasu kuwa sun ce 300 ne suka rasu a cikin kwanaki biyu zuwa uku.

"Da kaina na samu zantawa da masu aiki a ma'adanar gawawwaki da kuma makabartu. Na gano cewa an yi mace-macen amma sauyin yanayi ne ya kawo hakan.

"Hakan ke faruwa a jihohin Kano da Jigawa. Duk yankinmu daya.

"Amma zan iya sanar da ku kuma na tabbatar da cewa yawan mace-macen bai kai yadda ake fadi na," Tela yace.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya bayyana, mataimakin Gwamnan wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar, ya ce kafafen sada zumuntar zamani na ruwaito cewa mutum 300 ne suka rasu a mako daya.

Wannan ba gaskiya bane kuma ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da zancen.

A gefe guda, mun ji cewa Gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi ya sanar da garkame wasu kananan hukumomi guda uku a jahar Bauchi sakamakon bullar annobar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu na shekarar 2020 inda yace ya rufe garuruwan Katagum, Giade da kuma Zaki.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: An aiko wa Najeriya da maganin Madagascar

Bala ya danganta wannan mataki da ya dauka ga rahotannin da aka samu na mace mace a kananan hukumomin da kuma yaduwar cutar Coronavirus a cikinsu.

A dalilin yaduwar cutar da aka samu a kananan hukumomin Zaki, Giade da Katagum, adadin masu cutar Coronavirus a jahar Bauchi ya yi tashin gwauron zabi zuwa 181.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel