Mun bi sahun masu jinyar Coronavirus da su ka nemi su tsere – El-Rufai

Mun bi sahun masu jinyar Coronavirus da su ka nemi su tsere – El-Rufai

A ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, 2020, mu ka samu labarin cewa wasu Bayin Allah da aka yi wa gwajin kwayar cutar COVID-19 a jihar Kaduna, sun tsere sun bar gidajensu.

Gwamnatin jihar Kaduna karkashin Malam Nasir El-Rufai ta bada wannan sanarwa da kimanin karfe 1:00 na ranar Lahadi. Gwamnan ya ce wadannan mutane biyu sun yi dabo.

Wadannan mutane sun gudu ne bayan da aka sanar da su cewa su na dauke da cutar COVID-19, kuma za a bukaci a killace su a wani daki da aka tanada domin ayi masu magani.

Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa ya ba jami’an tsaro sunayen marasa lafiyan inda ya bukaci a nemo su a duk inda su ke, bayan an daina iya tuntubar su daga gidajensu.

Bayan kusan kimanin sa’a biyar da yin wannan magana kenan mai girma gwamnan ya tabbatar da cewa an yi nasarar gano wadannan marasa lafiya da su ka nemi su tsere a jiya.

KU KARANTA: Za a yi bincike a game da rashin bullar COVID-19 a Jihar Kogi

Gwamnan ya sake fitowa ya bada sanarwar cewa an bi sahun wadannan mutane kuma an gano su. Ana zarginsu da barin gidajensu bayan sunji cewa sun kamu da COVID-19.

El-Rufai ya ke cewa kwamishinar lafiya ta jihar Kaduna, Dr. Amina Mohammed-Baloni ta tabbatar da cewa an shigar da wadannan mutane biyu cikin dakin da ake killace masu cutar.

A jawabin da gwamnan ya yi, bai bayyana inda aka samu mutanen ba. Haka zalika gwamnan bai iya yin bayanin matakin da za a dauka game da gangancin wadannan Bayin Allah ba.

Kafin nan, gwamnan ya yi tir da wannan danyen aiki da talakawan sa su ka yi, ya ce akwai yiwuwar su gogawa wasu cutar. Ana sa ran cewa ba su gogawa kowa wannan cuta ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel