Tsohon ministan Shagari daga jihar Adamawa ya mutu
Tsoho sanatan Najeriya daga jihar Adamawa, Paul Wampana, ya mutu.
Rahotanni sun bayyana cewa Wampana ya mutu a cikin barcinsa da safiyar ranar Lahadi a gidansa Abuja, kamar yadda makusancinsa, Sylvester Ahmadu, ya shaidawa SaharaReporters.
Marigayin, wanda aka haifa a a garin Vimtim da ke karamar hukumar Mubi ta jihar Adamawa, ya taba rike shugaban majalisar dokokin tsohuwar jihar Gongola a jamhuriyya ta biyu.
Bayan kasancewarsa tsohon sanata mai wakiltar gabashin Adamawa, Wampana ya rike mukamin ministan lafiya lokacin mulkin tsohon shugaban kasa marigayi Shehu Shagari a shekarar 1983.

Asali: UGC
A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa, kwamishinan kasa da gidaje, Surajo Gatawa, ya mutu da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito a daren nan.
Jaridar ta ce wata majiya a gidan gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar kwamishinan, sai dai ta ce majiyar ba ta bayar da karin bayani ba.
DUBA WANNAN: Daga yanzu takunkumi ya zama dole a Kano, masu kunnen kashi zasu je kurkuku - Ganduje
.Wata majiya ta sanar da TheCable cewa an yi jan'izarsa da misalin karfe 7:00 na dare a gidansa da ke kan titin Sama daura da Babban Tanki a Sokoto.
Marigayin na daya daga cikin kwamishinoni 26 da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya nada a watan Nuwamba, 2018.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng