COVID-19: Ma'aikatan lafiya 47 sun harbu da cutar a Kano

COVID-19: Ma'aikatan lafiya 47 sun harbu da cutar a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da kamuwar ma'aikatan lafiya 47 da cutar coronavirus a jihar.

Shugaban kwamitin yaki da cutar na jihar Kano, Dr. Tijjani Hussain ya bayyana hakan a taron manema labarai a ranar Lahadi a garin Kano.

Hussain ya ce an gano ma'aikatan lafiyan sun kamu da cutar ne a makon da ya gabata amma ba a sake samun ma'aikatan lafiya da suka kamu da cutar ba a kwanakin nan.

Ya ce an samu wannan nasarar ne bayan kokarin gwamnatin jihar na gaggawa don bada kariya ga ma'aikatan lafiyan.

Hussain ya tabbatar da cewa mutum 576 aka tabbatar da suka dauke da cutar a jihar. An sallamin mutum 32 bayan an tabbatar da samun warakarsu.

COVID-19: Ma'aikatan lafiya 47 sun harbu da cutar a Kano
COVID-19: Ma'aikatan lafiya 47 sun harbu da cutar a Kano Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Daga cikin wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar a jihar Kano, an rasa rayukan mutum 21.

"A ranar Asabar, an samu mutum 84 wadanda ake zargin suna dauke da cutar. Hakan ya kai jimillar wadanda ake zargin suna dauke da cutar a jihar zuwa 1,820," yace.

Kamar yadda NTA ta bayyana, ya ce kwamitin dakile yaduwar cutar ta jihar ta samu kiran gaggawa 47 a ranar Asabar. Ta samu kira jimillar ya kai 1,313.

"A tsakanin ranakun Asabar zuwa Lahadi, 29 daga cikin samfur 84 da aka karba sun tabbata dauke da cutar.

"A halin yanzu mu karba samfur 2,072 a fadin jihar Kano," yace.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon ministan lafiya, Alhassan Halliru rasuwa

Hussain ya kara da cewa, daga cikin kokarin gwamnatin na tallafawa yayin annobar nan, sama da ma'aikatan lafiya 1,000 ake horarwa a jihar.

Ya yi kira ga jama'a da su kiyaye dokokin gujewa yaduwar cutar.

A wani labarin kuma, hukumar sauraron korafin alumma da yaki da rashawa na jihar Kano ta kama Shugaban karamar hukumar Kumbotso, Alhaji Kabiru Ado Panshekara a kan zarginsa da amfani da kujerarsa ba bisa kaida ba wurin rabon kayan tallafin da gwamnati ta bayar sobada kullen korona.

Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji Rimigado ya tabbatar da kama shugaban karamar hukumar a ranar Asabar kamar yadda New Telegrah ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel