Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon ministan lafiya, Alhassan Halliru rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon ministan lafiya, Alhassan Halliru rasuwa

- Allah ya yi wa tsohon ministan lafiya, Dr. halliru Alhassan rasuwa.

- Marigayi Halliru ya rasu yana da shekaru 66 a duniya.

- Ya rasu a yau Lahadi, 10 ga watan Mayun 2020 da karfe 12 na rana bayan gajeriyar rashin lafiya.

Allah ya yi wa tsohon ministan lafiya, Dr. halliru Alhassan rasuwa.

Alhassan Halliru ya rasu yana da shekaru 66 a duniya.

Ya rasu a yau Lahadi, 10 ga watan Mayun 2020 da karfe 12 na rana bayan gajeriyar rashin lafiya.

Alhassan, wanda aboki ne ga sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar, ya yi fama da ciwon sukari kafin rasuwarsa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, ya rasu ya bar mata daya da 'ya'ya hudu.

Wata majiya daga cikin iyalansa ta tabbatar da cewa za a binne shi a makabartar Hubbaran Shehu da ke garin Sokoto.

Kafin mutuwarsa, Dr Alhassan ya kasance shugaban, hukumar kula da harkokin lafiya ta jihar Sokoto.

Ya kuma kasance jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A wani labarin, kun ji cewa Allah ya yi wa mai bawa Gwamna Muhammadu Badaru shawara na musamman akan harkokin ilimin manya da na manyan makarantu, Ibrahim Ismail, rasuwa.

Marigayi Jarman Ringim kuma tsohon shugaban hukumar cigaban kananan hukumomi ya rasu ne a ranar Jumaa bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sanarwar rasuwar ta fito ne daga bakin babban mataimaki na musamman ga maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a sabbin kafafan sadarwa, Auwalu D. Sankara a shafinsa na Facebook.

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya yi ta’aziyya ga daukacin al’ummar da ke masarautar Ringim bisa rasuwar Alhaji Ibrahim Ismail Jarman Ringim wanda ya rasu ranar Jumaa bayan fama da rashin lafiya da ya yi.

KU KARANTA KUMA: Jigo a Izala, Sheikh Adam Muhammad, ya mutu

Alhaji Badaru da karshe yayi addua ga Allah subhanahu wata’ala da ya saka wa mamacin da aljanna firdausi kuma ya bai wa iyalan sa karfin gwiwar juriya da rashin da su kayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng