Korona ta sake hallaka mutane biyu a Kaduna

Korona ta sake hallaka mutane biyu a Kaduna

- Cutar Korona ta sake hallaka mutane biyu a Kaduna. Ya zuwa yanzu mutane uku kenan cutar ta hallaka a jihar

- Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya ce cutar korona ta sake kama wasu mutane biyu

- A daren ranar Asabar ne hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 239 a fadin Najeriya

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da mutuwar karin wasu mutane biyu da ke jinyar cutar korona, lamarin da ya mayar da adadin mutanen da suka mutu saboda annobar a jihar zuwa mutane uku.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya ce sabbin mutanen biyu da suka mutu sune; wani babban mutum daga karamar hukumar Makarfi da kuma wata mata daga karamar hukumar Zaria.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na tuwita, gwamnan ya ce an sake samun karin mutane biyu da suka kamu da kwayar cutar, lamarin da ya mayar da adadin masu korona a jihar zuwa mutane 87.

A cewar gwamnan, mutane biyun da suka kamu da kwayar cutar sun hada da wani namiji daga karamar hukumar Igabi da wata mace daga karamar hukumar Chikun.

A ranar 2 ga watan Mayu aka fara samun mutum na farko da cutar korona ta kashe a jihar Kaduna.

Marigayin, tsohon ma'aikacin gwamnati ne, da ya boye gaskiyar cewa ya yi bulaguro zuwa Kano. Ya mutu ne kafin sakamakon gwajinsa ya fito.

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:20 na daren ranar Asabar, 09 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 4151 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

DUBA WANNAN: Bawa kudi fifiko ne yasa Buhari bai bawa Ganduje biliyoyin da ya nema domin yaki da korona ba - Fadar shugaban kasa

An sallami mutane 745 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 128.

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 239 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:20 na daren ranar Asabar, 09 ga watan Mayu, 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel