Mbappe: Wenger ya ce ‘Dan wasan gaban Faransa ne zai karbi Ronaldo da Messi
Tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger ya na hangen matashin ‘dan wasa Kylian Mbappe ya yi wa Lionel Messi da Cristiano Ronaldo kafa a matsayin babban ‘dan kwallon Duniya.
Duk da cewa mutane su na ganin cewa Neymar Jr. ne zai gaji kambun babban ‘dan wasan duniya nan gaba, Arsene Wenger ya na ganin cewa Kylian Mbappe ne ‘dan wasan da ke gaba.
A na sa ra’ayin, Wenger wanda ya shafe shekaru 22 ya na horas da ‘yan wasan kungiyar Arsenal ya na ganin Kylian Mbappe ne zai gaji Messi da Ronaldo da su ke faman tashe tun 2008.
Wenger mai shekaru 70 ya sallama cewa Messi zakara ne maras tamka, sai dai duk da haka dattijon ya na cewa ‘dan wasan ya gama cin lokacinsa don haka zamaninsa zai shude.
“’Dan wasa Lionel Messi… ba mu taba ganin ‘dan wasan kwallo irinsa ba, wanda zai iya neman hanya a duk runtsin yanayi.” Wenger ya ke fadawa jaridar talkSPORT kwanan nan.
Arsene Wenger ya ke cewa a game da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo lokacinsu ya zo karshe a halin yanzu, don haka ya ce yanzu zamanin wasu sababbin jinin ‘yan kwallo za a shiga.
KU KARANTA: Sai Messi ya kai kusan shekaru 40 ya na taka leda - Xavi
"Yanzu ana maganar sababbin jini ne, kuma sababbin ‘yan wasan da za ayi yayi za su iya zama ‘Yan Faransa a wannan marra, jagoransu ka iya zama Kylian Mbappé.” Inji Wenger.
Bayan Wenger ya kira sunan Kylian Mbappé, sai kuma ya ce: “Haka zalika da kuma ‘dan wasa Neymar Jr. shi ma”. Jaridar talkSPORT ta fitar da wannan rahoto a karshen makon nan.
“Mun san cewa Ingila su na da dama sosai. Yanzu matasansu su na abin kirki. Sun yi kokari da Gareth Southgate a gasar cin kofin Duniya. Ina sa rai a fafata da su a gasar kofin Turai.”
Mbappé ya kafa tarihin kwallaye a gasar Ligue na kasar Faransa a bana. Kungiyarsa ta PSG ce ta lashe gasar shekarar nan. A 2018 kuma ‘dan wasan ya lashe gasar Duniya da Faransa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng