COVID-19: Za mu binciki lamarin Kogi da Kuros-Ribas inji Ministan lafiya

COVID-19: Za mu binciki lamarin Kogi da Kuros-Ribas inji Ministan lafiya

A ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu, 2020, Ministan lafiya watau Dr. Osagie Ehanire, ya tattauna da manema labarai kamar dai yadda 'yan kwamitin yaki da annobar COVID-19 su ka saba yi.

Dr. Osagie Ehanire ya shaidawa ‘yan jarida cewa za su tura tawagar kwararru na musamman domin su binciki ikirarin da wasu jihohi su ke yi na cewa ba su samu bullar COVID-19 ba.

Idan za ku tuna har yanzu ba a samu labarin mai dauke da kwayar cutar COVID-19 a jihohin Kogi da Kuros-Riba ba. Asali ma an ta samun matsala tsakanin jami’an NCDC da jihar Kogi.

Ministan lafiyan kasar ya tabbatar da cewa tawagar da aka tura zuwa Kogi sun gaza yin aikin da ya kai su. Ministan ya alakanta wannan matsala ne da sunan 'yan sabani da aka samu.

Osagie Ehanire ya ce za su sake aika ma’aikata da za su yi bincike game da laamarin jihar bayan matsalar da aka samu tsakanin gwamnatin jihar Kogi da jami’an gwamnatin tarayyar.

KU KARANTA: Abubuwa za su sukurkuce idan aka cire takunkumin zirga-zirga - Masana

A jawabinsa, mai girma ministan ya bayyana cewa: “Jihar Kogi ta na cikin jihohi biyu da su ka ce ba su da masu fama da COVID-19. Su na kokarin nuna cewa sun tabbatar da hakan.”

“Saboda haka yarjejiniyar da mu ka yi da su bayan tattaunawa da gwamnan ita ce, za mu tura tawaga su yi bincike su tabbatar mana da gaskiyar lamarin, su gana da hukumomi.”

"Mun yi kokarin aika tawaga zuwa Kogi a ranar Alhamis, amma an samu banbanci, za mu aika wata. Sai mun zauna da gwamna mun fada masa sharudan aikin gwamnatin tarayya.”

“Za mu yi wannan ne domin samun rahoto, sannan kuma mu iya fadawa Duniya halin da ake ciki a kasarmu.” Ministan ya ce ma’aikatar lafiya da hukumar NCDC za su karasa aikinsu.

A game da jihar Kuros Riba inda nan ma ake ikirarin annobar ba ta shiga ba, Osagie Ehanire ya ke cewa: “Haka zalika za mu tura tawaga zuwa jihar Kuros Riba a cikin mako mai zuwa.”

Cikin kokarin da ministan ya ce an yi, an aika ma’aikata da kayan aiki Kano da Katsina. An kuma shawo kan halin da ake ciki a Gombe, sannan ana binciken lamarin alamajirai a Jigawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng