COVID-19: Cire dokar zaman gida zai yi sanadiyyar kamuwar mutum miliyan 1.78

COVID-19: Cire dokar zaman gida zai yi sanadiyyar kamuwar mutum miliyan 1.78

Wasu masana daga jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, da ta Ahmadu Bello da ke Zariya da kuma jami’ar Lancaster ta Ingila sun fitar da wani bincike game da annobar COVID-19.

Hasashen wadannan gungun masana ya nuna cewa za a samu karuwar masu dauke da cutar COVID-19 idan har aka sassauta dokar zaman gida a garuruwan Legas da Kano nan gaba.

Binciken da kwararrun su ka yi ya bayyana cewa masu COVID-19 za su iya kai mutum miliyan 1.788 da zarar gwamnati ta cire takunkumin zaman gida a cikin watannin Yuni da Yuli.

A wannan bincike da aka gudanar, an fahimci cewa idan aka sassauta takunkumin da aka sa da 50%, masu dauke da COVID-19 a Kano za su zarce yawan adadin wadanda ke jihar Legas.

Binciken ya ce: “Idan aka kyale mutane su na barin gida su na fita cefane, su na zuwa aiki ana samun cakuduwa, adadin masu dauke da cutar a jihohin biyu zai tashi zuwa 748, 100.”

KU KARANTA: Gwamnati ta samu miliyoyin kudi na yaki da annobar COVID-19

Yusuf Yau Gambo da Yunus A. Abdulhameed su ka ce: “Za a iya samun mutane 102, 600 masu cutar a Legas, da kuma mutum 645, 500 a jihar Kano nan da farkon watan Yulin 2020.”

Wadannan malamai kwararru ne kan harkar lissafi a jami’ar ta Kano. Wadanda su ka duba aikin na su, su ne Farfesa Peter McClintock da Basant Kumar Jha na jami’ar Landan da A.B.U.

Binciken masanan ya na aiki ne da hasashe daga alkaluman hukumar NCDC. Kwarrun su ka ce idan har gwamnati ta cire dokar da ta sa na takaita zirga-zirga, abubuwa za su cabe a kasar.

A shawararsu, hanyar da za a iya bi kawai wajen hana yaduwar cutar kafin a kirkiro magani shi ne a takaita zirga-zirga. Binciken ya ce dole jama’a su hakura da ibadunsu da kuma al’adarsu.

Gambo da Abdulhameed sun bada shawarar cewa ka da gwamnati ta sassauta dokar zaman gida, a haramtawa mutane duk wata tafiyar da ba ta zama dole ba, sannan a rufe duk wuraren taro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel