COVID-19: Korona ta kashe wani fitaccen Dan Kasuwa a Yobe

COVID-19: Korona ta kashe wani fitaccen Dan Kasuwa a Yobe

Wani sanannen dan kasuwa a garin Nguru da ke jihar Yobe mai suna Alhaji Abdulhamid Nuhu na daga cikin mutanen da cutar coronavirus ta kashe a yau Asabar.

Kamar yadda SaharaReporters ta gano, lamarin ya kawo tsananin firgici a kananan hukumomin Nguru, Potiskum da Gashua inda suka tsorota sakamakon mace-macen da ya addabi yankin.

Mazauna yankin sun sanar da SaharaReporters cewa, mutane da yawa da suka rasu sun nuna alamomin cutar coronavirus.

Jama'ar sun tabbatar da cewa, duk da ci gaban mace-macen da ake yi, babu wani mataki da gwamnatin ta dauka na bincike ko daukar samfur don gano abinda ke kashe jama'a.

A tsakanin ranar 30 ga watan Maris zuwa yau 9 ga watan Mayu, daruruwan mutane sun rasu bayan nuna alamun cutar Covid-19.

A yayin zantawa a kan lamarin, daya daga cikin mazauna Nguru ya ce, "A kowacce rana mace-mace ake yi ana ci gaba da birne jama'a. Makabartunmu suna cika kuma duk muna cikin tsoro.

Korona ta kashe wani fitaccen Dan Kasuwa a Yobe
Korona ta kashe wani fitaccen Dan Kasuwa a Yobe. Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Allah ya yi wa Jarman Ringim Ibrahim Ismail, rasuwa

"Jihar Yobe ba ta da shugabanci na gari. A halin yanzu basu san me ya kamata su yi ba.

"Yobe na cikin dimuwa, rudani da tsoro. Gwamnatinmu bata da halin shawo kan wannan annobar. Kwamitin kula da yaduwar cutar duk masu son rashawa da wadanda basu san aiki ba aka tara. Ta kudi suke yi."

Akwai tsoron cewa cutar na yaduwa a tsakanin jama'a a jihar Yobe kuma rashin dakin gwaji da rashin niyyar samar da shi ne ke kawo yaduwar cutar.

Binciken da SaharaReporters ta gudanar ya bayyana cewa, dukkan manyan asibitocin da ke Nguru, Potiskum da Gashua suna cikin wani hali. Hakan ne yasa marasa lafiya ke shiga cikin mawuyacin hali.

Ma'aikatan lafiyan da ke manyan asibitocin gwamnati a Gashua, Nguru da Potiskum suna korafi a kan rashin kayayyakin kariya don duba marasa lafiya.

Amma kuma gwamnatin jihar Yobe ta musanta danganta mace-macen da ake da cutar korona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel