Matashi dan shekara 25 ya tsere daga cibiyar killace masu korona da ke jihar Bauchi

Matashi dan shekara 25 ya tsere daga cibiyar killace masu korona da ke jihar Bauchi

- Jami’ai daga hukumomi a jihar Bauchi sun ce suna kokarin gano inda wani mutum mai shekaru 25 yake da ya tsere bayan an tabbatar yana dauke da cutar COVID-19

- Wani jami’in gwamnati mai suna Rilwan Mohammed ne ya bayyana cewa an sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki

- Rilwan ya ce jami’an tsaro na ci gaba da neman mutumin a inda ake tunanin ya boye

A halin yanzu gwamnatin jihar Bauchi na kokarin gano wani mutum mai shekaru 25 da ya boye bayan an tabbatar da yana dauke da cutar COVID-19.

Shugaban cibiyar kiwon lafiya na jihar Bauchi, Rilwan Mohammed ya sanar da hakan ga jaridar Premium Times.

Ya ce mara lafiyan ya tsere daga cibiyar killacewa ta asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa.

Jami’in ya bayyana cewa bayanan sirrin da jami’an tsaron suka samu ya nuna cewa matashin mai shekaru 25 ya gudu zuwa karamar hukumar Darazo ta jihar.

Matashi dan shekara 25 ya tsere daga cikibiyar killace masu korona da ke jihar Bauchi
Matashi dan shekara 25 ya tsere daga cikibiyar killace masu korona da ke jihar Bauchi Hoto: Senator Bala A. Mohammed
Asali: Twitter

“Matashin mai shekaru 25 ya tsere tare da komawa Darazo. A halin yanzu ba a samo shi ba amma ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya na neman shi don dawo da shi,” Mohammed yace.

A wani labari na daban, shugaban kwamitin yaki da cutar korona na jihar Kano ya bayyana yadda ya warke da halin da ya fada yayin jinyar muguwar cutar.

Habib, wanda farfesa ne a jami’ar Bayero da ke Kano kuma ma’aikaci a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, ya warke a ranar 7 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Ba a sarki biyu a zamani daya: Wike ya yi wa shugaban 'yan sanda martani mai zafi

Kamar yadda takardar da ta fito daga ma’aikatar lafiya ta jihar ta bayyana, bayan jinyar da ya sha na kwanaki, gwaji ya nuna warakar da ya samu.

Malamin ya bayyana cewa ya samu cutar ne yayin da yake aiki da kwamitin yaki da cutar ta jihar Kano kuma ya sha jinyar wata daya cif.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel