Rikicin yanki: Mutum 50 sun bace, 300 sun samu raunika, da yawa sun rasa rayukansu

Rikicin yanki: Mutum 50 sun bace, 300 sun samu raunika, da yawa sun rasa rayukansu

Ana zargin rasa rayukan da ba su kirguwa a wani hargitsi da ya auku tsakanin yankin Omor da na Umumbo a karamar hukumar Ayamelum ta jihar Anambra.

An gano cewa, a kalla mutum 50 aka sace yayin da sama da manoma 300 suka samu miyagun raunika a fadan.

Kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana, an fara samun matsalar ne tun a lokacin ranin shekarar da ta gabata amma sai aka hanzarta yin sasanci.

Wani ganau ba jiyau ba, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce an tarwatsa tare da lalata wasu gidaje, shaguna da kamfanonin sarrafa shinkafa a Omor da kewaye.

Rikicin yanki: Mutum 50 sun bace, 300 sun samu raunika, da yawa sun rasa rayukansu

Rikicin yanki: Mutum 50 sun bace, 300 sun samu raunika, da yawa sun rasa rayukansu Hoto: Punch
Source: UGC

Kamar yadda ya bayyana, a lokacin da 'yan sanda suka isa yankin, an gano cewa a kalla mutum 50 ne aka sace, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, SP Haruna Mohammed, ya ce an tura rundunar 'yan sanda yankin don kawo karshen tashin hankalin.

KU KARANTA KUMA: Ba a sarki biyu a zamani daya: Wike ya yi wa shugaban 'yan sanda martani mai zafi

A wata takarda da ta fito daga gidan gwamnatin jihar wacce kwamishinan yada labarai na jihar, Mista C Don Adinuba yasa hannu, ya ce hargitsin ya biyo bayan kin duba kokarin gwamnati ne da jama'ar jihar suka yi na kusan shekaru shida don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A gefe guda, wasu gungun miyagu yan bindiga sun yi kutse a gidan wani magidanci dake kauyen Tarkende cikin garin Umenger, na karamar hukumar Guma a jahar Benuwe a daren Laraba.

A yayin wannan kutse da miyagun suka yi, sun kashe maigidan da matarsa wanda take dauke da juna biyu ta hanyar bude musu wuta, inda suka musu ruwan harsashi babu gaira babu dalili.

Daily Trust ta ruwaito mazauna kauyen sun bayyana cewa suna barci karar harbin bindiga ya tashe su a firgice kowa ya yi ta kansa don neman tsira, a sanadiyyar haka wasu sun jikkata.

Shugaban karamar hukumar Guma, Anthony Shawon ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace yan bindigan sun kashe miji da mata, sa’annan yan garin da dama sun jikkata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel