Makashin maza: Sojoji sun halaka ‘Orjondu’ da suka dade suna farautarsa wurjanjan a Benuwe

Makashin maza: Sojoji sun halaka ‘Orjondu’ da suka dade suna farautarsa wurjanjan a Benuwe

Zaratan dakarun rundunar Sojin Najeriya dake jibge a jahar Benuwe sun samu nasarar halaka Terugwa Igbagwa, kasurgumin dan bindiga da suka dade suna farautarsa ruwa a jallo.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito shugaban sashin watsa labaru na shelkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Miji ya watsa ma matarsa tafasashshen ruwan zafi a kan zarginta da cin amana

Enenche yace Terugwa Igbagwa inkiya Orjundu ya gamu da ajalinsa ne a wani karan batta da suka yi da miyagun a mafakarsu dake kan hanyar Zaki Biam zuwa Katsina-Ala a Benuwe.

Ya kara da cewa Sojojin da suka kai harin sun hada da dakarun Operation Whirl Stroke Tracking Team da dakarun Special Forces na shiyya ta 2 dake garin Zaki Biam.

Makashin maza: Sojoji sun halaka ‘Orjondu’ da suka dade suna farautarsa wurjanjan a Benuwe

Orjondu Hoto: Nairaland
Source: UGC

“A wannan samame muka kashe Terugwa Igbagwa mai inkiya Orjondu, idan za’a tuna Orjondu ne mutum na biyu mafi girma da muke farauta wurjanjan a jahar Benuwe bayan Gana.” Inji shi.

Enenche ya ce Orjondu ne kanwa uwar gami a satar mutane, fashi da makami, kashe kashen mutane, safarar bindigu da sauran miyagun ayyuka a yankin Katsina Ala, Ukum da Logo.

Sojojin sun gano bindigar AK 47 da wasu bindigu kirar gida, alburusai da dama da kuma layu a mafakar miyagun.

Daga karshe Enenche ya bayyana cewa shugabancin Sojin Najeriya na jinjina ma dakarun Operation Whirl Stroke sakamakon nasarar da suka samu.

A wani labarin kuma, gungun yan bindiga sun yi kutse a gidan wani magidanci dake kauyen Tarkende cikin garin Umenger, na karamar hukumar Guma a jahar Benuwe a daren Laraba.

A yayin wannan kutse da suka yi, sun kashe maigidan tare da matarsa wanda take dauke da juna biyu ta hanyar bude musu wuta, inda suka musu ruwan harsashi babu gaira babu dalili.

Daily Trust ta ruwaito mazauna kauyen sun bayyana cewa suna barci karar harbin bindiga ya tashe su a firgice kowa ya yi ta kansa don neman tsira, a sanadiyyar haka wasu suka jikkata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel