COVID-19: Gwamna ya yi umurnin yin gwanjon motocin da aka kama suna karya dokar kulle

COVID-19: Gwamna ya yi umurnin yin gwanjon motocin da aka kama suna karya dokar kulle

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce za a yi gwanjon motocin da aka kama masu shi suna tuka su a lokacin dokar hana fita a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu, a wata hira bayan ya fita rangadi don ganin yadda ake bin dokar da gwamnati ta saka, Channels TV ta ruwaito.

“Kotun tafi-da-gidanka za ta hukunta wadanda suka karya dokar kuma na fada ma Atoni Janar, ya zama dole a yi gwanjon dukkanin ababen hawan da aka kama.

"Zuwa gobe, mai girma Atoni Janar zai tallata ababen hawan kuma za mu yi gwanjon su,” in ji shi.

“Wasu mutane ba su yarda cewa akwai coronavirus ba. Har sai an fahimtar da su cewa da gaske muke, ba za su yarda ba. Za mu yi gwanjon motocin da aka kama.

“Wadanda aka kama za su fuskanci doka. Babu wanda ya fi karfin doka. Ba za mu bari wani ya bata kokarin da muke na kare mutanenmu ba.”

COVID-19: Gwamna ya yi umurnin yin gwanjon motocin da aka kama suna karya dokar kulle
COVID-19: Gwamna ya yi umurnin yin gwanjon motocin da aka kama suna karya dokar kulle Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Yayinda yake kula da yadda mutane ke bin dokar, Gwamna Wike ya sa an kama wasu da dama da suka karya doka da kuma kwace motoci.

KU KARANTA KUMA: Yadda korona ta kashe dan majalisa a Borno - Iyalansa (Hotuna)

Wasu daga cikin wadanda aka kama sun kasance manyan mutane, wadanda ba su kasance daga cikin mutanen da aka yarda su fita ba, amma kuma sai suka fito da yan sandan da ke tsaron su.

Sai dai kuma gwamnan ya kyale wata mai juna biyu da ta karya doka saboda tausaya mata.

A cibiyar killace masu cutar na Elekahia, an kama sama da mutane 200 sannan an kwace motoci sama da guda 20.

A gefe guda, gwamnatin jihar Yobe ta yi martani game da rahotannin mace macen da ake samu a jihar cikin sati daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa fiye da mutum 100 ne suka mutu cikin sati daya bisa la'akari da alkalluman da aka samu daga garurruwan Potiskum, Gashu’a da Nguru.

Mataimakin shugaban kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a jihar wadda shine kuma kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Muhammad Lawan Gana ya ce gwamnatin za ta yi bincika gawarwakin wadanda suka mutu don gano dalilin mace-macen a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel