Korona: Ta harbi karin mutane 381, 55 a Kano, 44 a Jigawa, 19 a Bauchi

Korona: Ta harbi karin mutane 381, 55 a Kano, 44 a Jigawa, 19 a Bauchi

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 381 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:20 na daren ranar Alhamis, 07 ga watan Mayu, 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 381 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

183-Lagos

55-Kano

44-Jigawa

19-Zamfara

19-Bauchi

11-Katsina

9-Borno

8-Kwara

7-Kaduna

6-Gombe

5-Ogun

4-Sokoto

3-Oyo

3-Rivers

2-Niger

1-Akwa Ibom

1-Enugu

1-Plateau

Alkaluman NCDC na ranar Alhamis sun nuna cewa an samu hauhawar lambobin mutanen da suka kamu da cutar a jihohin arewacin Najeriya, musamman jihohin arewa maso yamma da arewa maso gabas.

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:20 na daren ranar Alhamis, 07 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 3526 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

DUBA WANNAN: An bawa hammata iska a kan gawar mahaifiyar Buratai

An sallami mutane 601 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 107.

Daga cikin mutanen da aka sallama akwai mutane 16 da suka warke sarai bayan sun yi jinyar cutar a cibiyar killacewa da ke Kano.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammed Garba, ya tabbatar da sallamar mutanen a cikin wani jawabi da ya fitar da yammacin ranar Alhamis.

Daga cikin mutanen da aka sallama akwai Farfesa Abdulrazak Garba Habeeb na sashen koyar da aikin likita a jami'ar Bayero da kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel