Korona ta hallaka likita a jihar Borno

Korona ta hallaka likita a jihar Borno

Wani kwararren likita ya mutu a asibitin koyarwa (UMTH) na jami'ar Maiduguri bayan ya kamu da kwayar cutar covid a jihar Borno, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

Kwararren likitan mai suna Mohammed Kumshe ya mutu ne ranar Alhamis a bangaren killace masu jinyar korona a asibitin.

SaharaReporter ta bayyana cewa likitan ya kamu da kwayar cutar ne bayan ya yi mu'amala da wani mai cutar.

Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasa (NCDC) ta ce ya zuwa yanzu akwai jimillar mutane 116 da aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar a jihar Borno.

Korona ta hallaka likita a jihar Borno
Marigayi Mohammed Kumshe Hoto: SaharaReporters
Asali: UGC

Daga jihar Yobe, mai makwabtaka da jihar Borno, wasu manyan mutane uku da suka yi suna sun mutu a cikin sa'a 24 daga cutar da ake zargin cewa annobar korona ce jihar Yobe, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

Manyan mutane sune; tsohon mamba mai wakiltar Nguru/Machina/Karasuwa/Yusufari a majlisar wakilai ta kasa, Alhaji Baba Bukar Machina, Muazu Buraji, darektan ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe, da Alhaji Bana Kura, wani sanannen ma'aikacin gwamnati a Geidam.

Machina ya mutu ne a cibiyar killacewa a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, kuma za a binne shi ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: An bawa hammata iska a kan gawar mahaifiyar Buratai

Da SaharaReporters ta tuntubi Mamman Mohammed, darektan yada labarai da kafafen sadarwa a Yobe, ya ce bashi da masaniya a kan abinda ya ke faruwa,

Ya bayyana cewa kwamishinan lafiya na Yobe zai gabatar da jawabi ga manema labarai a kan halin da ake ciki a jihar.

A ranar Laraba ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa a kalla mutum 155 ne su ka mutu a cikin kwanaki 6 a kananan hukumomin Gashua da Potiskum da ke jihar Yobe.

A cewar jaridar SaharaReportes, mutanen na nuna alamu da ke kama da na ma su dauke da kwayar cutar covid-19 kafin su mutu.

Yawaitar mace - macen, wacce ke kama da irinta jihar Kano, ta jefa tsoro da zaman zulumi a tsakanin mazauna kananan hukumomin.

Wani kwamitin bincike da shugaban kasa ya tura Kano ya alakanta yawaitar mutuwar mutanen jihar da annobar covid-19.

Wata majiya ta sanar da SaharaReporters cewa a kalla mutane 98 ne su ka mutu a karamar hukumar Potiskum a tsakanin ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, zuwa ranar Talata, 5 a watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel