Annobar Coronavirus: Israila ta baiwa Najeriya taimakon kayan kariya 2,000
Ofishin jakadancin kasar Israila a Najeriya ta mika ma gwamnatin Najeriya kayan kariyan fuska guda 2,000 a matsayin gudunmuwa ga ma’aikatan kiwon lafiya don yaki da Coronavirus.
Jaridar Punch ta ruwaito jakadan Israila a Najeriya Shimon Ben Shoshan ne ya mika kayan ga ministan lafiya Osagie Ehanire a ranar Alhamis, inda yace a Najeriya suka kera kayan.
KU KARANTA: Amfani da Chloroquine: Duk lalube muke yi a cikin duhu – Gwamnan Bauchi
“Wannan wani abu ne da muka dade muna yi, tun kafin barkewar annobar COVID-19, shine gudanar da kirkire kirkiren kiwon lafiya na kasar Israila a Najeriya, abin da muke gani a yau shi ne wani aikin hadin gwiwa tsakanin kamfanonin Israila da kamfanonin Najeriya wajen hada kariyan fuskan.
“A kasar Israila muka tsara kariyan fuskan, amma a Najeriya muka kera shi, wannan shi ne gudunmuwar Israila ga Najeriya, burinmu mu bayar da guda 10,000 don amfanin ma’aikatan lafiya dake yaki da COVID-19.
“Wannan kashi na farko ne guda 2,000, za mu cigaba da aikin samar da sauran, kuma zamu mika su nan bada jimawa ba, kawai dai muna daukan tsawon lokaci ne kafin a kammala aikin.” Inji shi.
Shimon ya ce cutar Coronavirus da aka samu a Najeriya bai kai wanda aka samu a kasar Israila ba, inda mutane 16,500 suka kamu tare da mutuwar mutane 237.
Da yake amsan kayan, Minista Ehanire ya bayyana godiyar Najeriya ga kasar Israila, jakadan kasar da kuma tawagarsa bisa wannan gudunmuwa da suka bayar.
“Taimakon ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa, za mu yi farin cikin amfani da kariyan fuskan saboda akwai lokutta da dama da muke bukatar amfani da su. Zamu aika su ga wadanda suka fi bukatarsu a duk fadin kasar nan.” Inji shi.
A wani labari kuma, Ministan lafiya, Mista Osagie Ehanire ya ce a shirye gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take ta yi amince da maganin gargajiya don yaki da Coronavirus.
Sai dai Ministan ya ce amma fa dole ne maganin gargajiyan ya samu tantancewa tare da amincewa daga cibiyar binciken magunguna da cigabansu ta Najeriya, NIPRD.
A cewarsa, duk wani boka ko mai maganin gargajiya da ya yi ikirarin gano maganin Coronavirus ya tafi NIPRD don samun takardar amincewa kafin a yi gwajin maganin.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng