Yanzu-yanzu: Gwamna Tambuwal ya yi babban rashi

Yanzu-yanzu: Gwamna Tambuwal ya yi babban rashi

- Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da rasuwar kawun Gwamna Aminu Tambuwal, Sheikh Haruna Waziri Usman

- Babban malamin ya rasu ne a yau Alhamis, 7 ga watan Mayun 2020 yayin da yake da shekaru 96 a duniya

- Gwamnan ya bayyana alhininsa tare da fawwala wa Allah lamuransa, ya yi addu'ar neman gafara da kuma aljanna ga shehin malamin

Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da rasuwar kawun Gwamna Aminu Tambuwal, Sheikh Haruna Waziri Usman.

Babban malamin ya rasu yana da shekaru 96 a duniya, kamar yadda SaharaReporters ta wallafa.

Gwamnatin jihar ta sanar da babban rashin ne ta wata takarda da ta fito daga mai bada shawara na musamman ga gwamnan a kan yada labarai, Muhammad Bello a ranar Alhamis 7 ga watan Mayu.

Kamar yadda takardar ta bayyana, "Cike da alhini tare da fawwala wa Allah al'amura, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto na sanar da rasuwar kawunsa, Sheikh Haruna Waziri Usman.

"Sheikh Haruna ya rasu a garin Tambuwal yana da shekaru 96 a yau Alhamis, 7 ga watan Mayu.

"Gwamna Tambuwal na fatan Allah ya yafe masa tare da saka shi a Jannatul Firdaus. Yana kira ga jama'ar jihar da su tsananta addu'a ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

"Ya kara da fatan Allah ya ba marasa lafiyar jihar lafiya mai daurewa."

Yanzu-yanzu: Gwamna Tambuwal ya yi babban rashi
Yanzu-yanzu: Gwamna Tambuwal ya yi babban rashi. Hoto daga SaharaReporters
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kano: Yadda 'yan sanda suka hana dubban mutane shiga Kasuwar Kwari

A wani labari na daban, jami'an tsaro sun hana dubban yan kasuwa da masu cin kasuwa shiga kasuwar sayar da tufaffi na Kwari da ke Kano a yayin da gwamnatin jihar ta sassauta dokar kulle da ta saka a baya don dakile yaduwar korona.

Idan za a tuna Gwamna Abdullahi Ganduje a makon da ya gabata ya sanar da cewa kasuwannin Yan Kaba da Yan Lemo ne kawai aka bawa damar budewa a ranakun Litinin da Alhamis.

An kuma bawa wasu manyan kantina damar budewa domin sayar wa alumma kayan masarafi a ranakun biyu daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel