An samu korona a jikin 'yan Lebanon 25 da suka koma kasarsu daga Kano

An samu korona a jikin 'yan Lebanon 25 da suka koma kasarsu daga Kano

Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce mutum 25 ne a jirgin da ya sauka kasar daga Kano a ranar Laraba ke dauke da cutar coronavirus.

A watan Afirilu yayin farkon cutar a kasar, gwamnatin kasar Labanon ta bukaci kamfanin jiragen sama na gabas ta tsakiya da ya kwaso mata 'yan kasar ta da ke kasashen ketare.

"A ranar 5 ga watan Afirilu, kamfanin jirgin saman ya sanar da cewa zai kwaso mata 'yan kasarta kamar yadda ta bukata," takardar da ta fito daga kamfanin jiragen saman ta sanar a ranar 3 ga watan Afirilu.

Kamar yadda jaridar The Cable ta bayyana, jirgin da ya taso a ranar 5 ga watan Afirilu daga jihar Kano zuwa Beirut ya sauka a kasar.

An samu korona a jikin 'yan Lebanon 25 da suka koma kasarsu daga Kano
An samu korona a jikin 'yan Lebanon 25 da suka koma kasarsu daga Kano Hoto: TheCable
Asali: UGC

Amma takardar da ta fito daga ma'aikatar lafiya ta kasar ta tabbatar da cewa fasinjoji 25 ne suke dauke da cutar COVID-19.

Takardar ta kara da cewa an garzaya da fasinjoji asibiti tun bayan saukarsu sannan an killace sauran da basu dauke da cutar.

Ma'aikatar lafiya ta ce idan fasinjojin da suka bayyana basu dauke da cutar suka nuna wata alama ta COVID-19, za a mayar dasu asibiti don sake gwajin.

"Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa mutum 25 daga cikin 'yan kasar da aka kwaso daga Kano ke dauke da cutar COVID-19.

"An mika wadanda abun ya shafa asibiti yayin da aka killace sauran. Duk wanda aka samu da wata alamar cutar, za a kai shi asibiti don sake gwajin."

KU KARANTA KUMA: An kama wasu Kanawa 40 a hanyarsu ta yin kaura zuwa Legas

Kamar yadda ma'aikatan lafiya ta kasar Lebanon ta bayyana da karfe 11:30 na safiyar Alhamis, kasar na da majinyata 784 da ke dauke da muguwar cutar.

A wani labarin kuma, jami'an tsaro sun hana dubban yan kasuwa da masu cin kasuwa shiga kasuwar sayar da tufaffi na Kwari da ke Kano a yayin da gwamnatin jihar ta sassauta dokar kulle da ta saka a baya don dakile yaduwar korona.

Idan za a tuna Gwamna Abdullahi Ganduje a makon da ya gabata ya sanar da cewa kasuwannin Yan Kaba da Yan Lemo ne kawai aka bawa damar budewa a ranakun Litinin da Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel