An kama wasu Kanawa 40 a hanyarsu ta yin kaura zuwa Legas
A kalla matafiya 40 ne da ke kan hanyar zuwa Legas daga Kano aka tare a jihar Niger, jaridar The Punch ta ruwaito.
Wannan na kunshe a wata takarda da Mary Noel-Berje, sakatariyar yada labarai ta Gwamna Abubakar Bello ta sa hannu.
Kamar yadda takardar ta bayyana, an kuma kama wasu fasinjojin 19 sun fito daga jihar Legas za su tafi Kano sai kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar Niger suka taresu.
Jihar Niger na yankin Arewa ta tsakiya a Najeriya kuma tana daga cikin jihohin da suka hada yankin Arewa da kudancin kasar nan.

Asali: UGC
A ranar Litinin 27 ga watan Afirilu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin hana zirga-zirga tsakanin jihohin Najeriya har sai yadda hali yayi.
An tabbatar da wannan dokar ne don hana yaduwar annobar coronavirus a tsakanin jama'a.
"Duk da rufe iyakokin jihohi da aka yi, jama'a na yin amfani da kowacce dama suka samu don yawo. Abun mamaki ne ka ga jama'a na yawo a kasan tamfal da buhunan shinkafa.
"A bangarenmu, ba za mu bar wata damar da za su yi amfani da ita. Dole ne su koma inda suka fito," Kwamishinan lafiya na jihar Niger, Dr Muhammad Makusidi, ya sanar.
Gwamnatin ta ce duk wanda aka kama za a yi mishi hukunci ne a kotu tafi-da-gidanka. Hukuncin zai kama daga watanni uku ko shekara daya a gidan kaso.
KU KARANTA KUMA: Kano: Yadda 'yan sanda suka hana dubban mutane shiga Kasuwar Kwari
Jihar Legas na da mutum 1,308 da aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar. Jihar Kano na da mutum 427 kuma ita ce jihar da ta fi yawan masu cutar a yankin Arewa kamar yadda hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta sanar a daren Laraba.
A gefe daya, a ranar Alhamis ne ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da karin mutuwar majinyata 5 da ke fama da cutar coronavirus a jihar.
A wani rubutu da aka wallafa a shafin Twitter na ma'aikatar lafiyar, ta tabbatar da sallamar wasu mutum uku da suka warke daga cutar.
Mutuwar mutum biyar din an sanar da ita ne da safiyar Alhamis kamar yadda NCDC ta sanar a daren ranar Laraba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng