Za a watsa N2tr a cikin tattali arziki a lokacin annobar COVID-19 - Minista

Za a watsa N2tr a cikin tattali arziki a lokacin annobar COVID-19 - Minista

Ganin yadda annobar cutar Coronavirus ta jefa kasashen duniya a cikin matsala, gwamnatin tarayya ta Muhammadu Buhari ta fara tunanin yadda za ta ceci tattalin arzikin Najeriya.

Jaridar Business Day ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya na sa ran zuba Naira tiriliyan biyu a cikin tattalin arziki. Gwamnati ta na sa ran dumbuza wannan kudi nan ba da dadewa ba.

Karamin ministan kudi, Clem Agba ya bayyana cewa gwamnati ta na neman hanyar zuba kudi a cikin tattalin arziki domin a ceto kamfanoni da ma’aikatan da su ka shiga cikin matsala.

Gwamnatin Najeriya ta na tunanin agazawa ma’aikatan da ke aiki a kamfanonin jirgi da filayen tashi da saukar jirgin sama, wanda wannan annoba ya sa abubuwa su ka tsaya masu cak.

Ministan ya ke cewa kamfanonin jiragen sama su na tafka asarar fiye da Naira biliyan 20 duk wata sakamakon annobar Coronavirus da ta sa aka hana jirage shigowa da barin Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta rage farashin litar fetur a tashohin mai

Za a watsa N2tr a cikin tattali arziki a lokacin annobar COVID-19 - Minista

Karamin Ministan tattali arziki Clement Agba
Source: Twitter

Kwamitin bunkasa tattalin arziki ne zai kawo hanyar da za a bi wajen ceto tattalin kasar. Clem Agba ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro da aka yi a babban birnin tarayya Abuja.

Premium Times ta ce idan har wannan ya tabbata, kudin za su fito ne daga babban bankin CBN, da bankin bunkasa kasuwanci da tallafin da Najeriya za ta samu daga kasashen waje.

Bayan farashin danyen mai ya yi raga-raga a kasuwa, gwamnatin Najeriya ta yi maza ta rage burin da ta ci daga man fetur, ta canza lissafin abin da za a samu daga kudin gangar mai.

Annobar COVID-19 ta taba farashin mai har ta kai Ministar kudi da tattalin arziki da tsare-tsaren kasafin kasa, Zainab Ahmed ta bada sanarwar cewa za a rage 15% daga cikin kasafin bana.

Jihohin kasar za su samu tiriliyan guda a matsayin kasonsu daga wannan kudi da za a watsa a tattalin arzikin. Kawo yanzu ba a kai ga cin ma matsaya game da wannan mataki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel