NBET: Gwamnatin Tarayya ta amince da nadin Shugaba da Darektoci

NBET: Gwamnatin Tarayya ta amince da nadin Shugaba da Darektoci

- Shugaban kasa Buhari ya nada sababbin shugabannin kamfanin NBET

- Marilyn Amobi za ta cigaba da rike kujerar shugabar kamfanin wutan

- Ministar kudi ce za ta jagoranci Darektocin da za su sa ido a kamfanin

A yau Alhamis, 7 ga watan Mayu, 2020, fadar shugaban kasar Najeriya ta bada sanarwar cewa an yi wasu sauye-sauye a hukumar NBET da ke karkashin ma’aikatar wutar lantarki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da Marilyn Amobi a matsayin shugabar NBETE, sannan ya amince da nadin wasu sababbin manyan darektoci da za su sa ido a kamfanin.

Shugabar majalisar darektocin da za su rika lura da aikin wannan kamfani ita ce ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed Shamsuna. Akwai wasu mutum shida da za su taimaka mata.

Sauran darektocin da aka nada sun hada da Alex Okoh, wanda aka zakulo daga ma’aikatar BPE.

A cikin wannan majalisa ta darektoci akwai shugabar hukumar DMO, Patience Oniha.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya amince da nadin sabon Shugaban hukumar NAICOM

Babban darektan ofishin kasafin kudi na kasa, Ben Akabueze ya na cikin wadanda za su ido a kamfanin. Akwai tsohon shugaban kungiyar NSE, Injiniya Musatafa Balarabe Shehu.

Mustapha Shehu zai zama darekta mai zaman kansa wanda ya fito daga wajen gwmanati. Sai kuma tsohon shugaban hukumar SEC, Suleymen Ndanusa ya na cikin darektocin.

Har ila yau shugaban kasa ya sa Adeyeye O. Adepegba a matsayin darekta mai zaman kansa. Dr. Marilyn Amobi ita ce shugaba watau CEO na kamfanin saida wutar lantarkin kasar.

Kwanakin baya an yi ta samun matsala tsakanin Marilyn Amobi da ministar wuta. Shugabar kamfanin ta yi karatu a Najeriya da Landan, kuma ta kware a sha’anin aikin lantarki.

Idan za ku tuna a 2010 aka kafa wannan kamfani wanda ke da alhakin sayen wutar lantarki a kan sari daga hannun ‘yan kasuwa, ya kuma saidawa masu amfani da wuta a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel