Cutar coronavirus ba ta kashe kowa ba a jihar Yobe – Gwamna Mala Buni

Cutar coronavirus ba ta kashe kowa ba a jihar Yobe – Gwamna Mala Buni

Gwamnatin jihar Yobe ta tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa a jihar sakamakon annobar Coronavirus.

Gwamnatin jihar ta sanar da hakan ne yayin da take martani a kan rahoton yawan mace-macen da aka ce ana yi a jihar.

Kamar yadda wata takarda da ta fita a ranar Alhamis, Mamman Mohammed, mataimaki na musamman ga gwamna Mai Mala Buni a fannin yada labarai, ya ce an fara samun bullar cutar ne a karon farko a makon da ya gabata a jihar.

Cutar coronavirus bata kashe kowa ba a jihar Yobe – Gwamna Mala Buni
Cutar coronavirus bata kashe kowa ba a jihar Yobe – Gwamna Mala Buni
Asali: UGC

Mohammed ya sake musanta ikirarin da ake yi na cewa Buni ya bar jihar inda ya koma Abuja.

Ya ce gwamnan ya tafi babban birnin tarayyar ne don ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewarsa"Jihar Yobe ce ta fara aika wa da samfur na wanda take zargin yana dauke da cutar amma aka yi sa'a baya dauke da ita," .

"Duk da ba a samu cutar a jihar ba, gwamnatin ta kafa kwamitin COVID-19, ta samar da cibiyar killacewa tare da duk kayayyakin aikin da ya dace.

"An fara samun bullar cutar a jihar Yobe a ranar 30 ga watan Afirilun 2020 amma kuma babu wanda ya taba rasuwa sakamakon cutar.

"Abu na biyu, Gwamna Buni bai fita jihar ba na tsawon makonni shida har sai da shugaba Buhari ya gayyacesa Abuja don tattaunawa a kan lamarin tsaro na jihar. Kwanaki uku kacal ya yi kuma ya dawo Yobe.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya hana huldar kasuwanci ko wata ma'amala da duk wanda ba jihar yake ba

"Don haka, yana nan cikin jihar yana mulkinsa ba kamar yadda ake ta rade-radi ba.

"Gwamnatin jihar na kira ga manema labarai da su nemi sani ko karin bayani a kan kowanne lamari kafin a wallafa ko yadawa."

A halin yanzu, jihar Yobe na da mutum 13 da aka tabbatar suna dauke da muguwar cutar.

A gefe guda, mun ji cewa tsohon kwamishan ayyuka na jihar Kano, Muazu Magaji, ya kamu da cutar Coronavirus.

Muazu Magaji da kanshi ya bayyana hakan da safiyar Alhamis, 7 ga Mayu, 2020 a shafinsa na Facebook.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel