Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya hana huldar kasuwanci ko wata ma'amala da duk wanda ba jihar yake ba

Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya hana huldar kasuwanci ko wata ma'amala da duk wanda ba jihar yake ba

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya umarci mazauna jihar da su yanke huldar kasuwanci ko wata ma'amala da duk wanda ba jihar yake ba.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito, Mohammed ya sanar da hakan ne yayin wani taro da ya yi da shugabannin kananan hukumomin jihar.

Ya ce yadda cutar korona ke ci gaba da yaduwa a jihohin da ke makwabtaka da Bauchi abin tashin hankali ne. Don haka akwai bukatar shugabannin su wayar da kan jama'arsu a kan gujewa mu'amala da kowa a wajen jihar.

"Har yanzu muna cikin damuwa saboda yadda jama'a ke shigowa jihad nan. Mun samu labarin cewa a Jigawa an samu mutum 46 da suka kamu a rana daya.

"Jihar Kano kuwa kowa hankalinsa ya koma kansu. Muna jajantawa jam'ar jihar Kano a kan mace-macen da suke fuskanta.

"Mun sanar da shugabannin kananan hukumomi cewa babu wani dan kasuwa, bako ko wata mu'amala da za a dinga yi da jama'ar da ba na jihar Bauchi ba," gwamnan yace.

Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya hana huldar kasuwanci ko wata ma'amala da duk wanda ba jihar yake ba

Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya hana huldar kasuwanci ko wata ma'amala da duk wanda ba jihar yake ba
Source: Twitter

Ya dora nauyin kula da yanayin tsaron yankuna a kan kwamitin rikon kwarya na shugabannin kananan hukumomi don bada kariya ga rayukan jama'a.

Ya kara da kafa kwamitin wayarwa da sa ido a kowanne yanki tare da bukatar su samar da takunkumin fuska masu tarin yawa.

"Kwamitin da muka kafa na ayyuka ne kuma dole su fita aiki don samar da takunkumin fuska ga jama'ar jihar.

"Jihar mu za ta ci gaba da zama a kulle komai kuwa ke faruwa a wasu wurare," ya kara da cewa.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Kano ta sake samun karin mutum biyar da suka mutu

A yayin da Gwamna Mohammed ke magana a kan karewar wa'adin mulkin kwamitin rikon kwaryar, ya ce an kara musu lokaci tuna ba za a iya zabe ba a lokacin da ake tsaka da annobar nan ba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon kwamishan ayyuka na jihar Kano, Muazu Magaji, ya kamu da cutar Coronavirus.

Muazu Magaji da kanshi ya bayyana hakan da safiyar Alhamis, 7 ga Mayu, 2020 a shafinsa na Facebook.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel