Kudin litar fetur a manyan tashoshin mai ya koma N108 – PPMC

Kudin litar fetur a manyan tashoshin mai ya koma N108 – PPMC

- NNPC ta ce an maida kudin litar fetur a tashar mai ya zama N108

- Hukumar PMMC ce ta sanar da ragin N5 domin a bunkasa ciniki

- Ba a tabbata ko hakan zai sa kudin fetur ya ragu a gidajen mai ba

A ranar Laraba, 7 ga watan Mayu, 2020, kamfanin man fetur na Najeriya watau NNPC ya bada sanarwar rage farashin fetur a manyan tashoshin mai daga N113.28 zuwa N108.

Babban jami’in NNPC da ke kula da yada labarai, Kennie Obateru ya fitar da wannan sanarwa, ya na mai dogara da jawabin da shugaban kamfanin PPMC, Musa Lawan ya yi.

Kamfanin NNPC ya yi wannan ragi na Naira biyar ne a kan kowane lita a tsakiyar makon nan. Kamfanin ya ce rage kudin litar na fetur ya na cikin dabarun kasuwancinsu.

Musa Lawan ya ce sun yi wannan dabara ne domin su rika samun ciniki sosai a kasuwa tare da bin sharudan da hukumar PPPRA mai lura a farashin kayan mai da gindaya a kasar.

KU KARANTA: Gwamnati ta rage kudin mai a karo na biyu a cikin kwanaki

Da ake bada sanarwar rage kudin, kamfanin ya ce wannan ragi zai yi tasiri a duk wasu tashoshin man da ke fadin kasar, sabon farashin zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba.

Da wannan canjin kudin da aka samu, PPMC za ta bunkasa cinikinta, har ta saida tarin gangunan man da ta tara. Za a saida fetur ga miliyoyin mutanen kasar a farashi mai sauki.

Lawal ya ce PPMC ta cin ma wannan sabon farashi ne bayan ta yi nazarin yadda kasuwa ta ke tafiya. Sashen da ke lura da farashin mai ne ya yi wannan aiki a madadin hukumar.

Sai dai hukumar ba ta bayyana ko wannan ragin farashi da aka yi a tashohin man zai kai ga raguwar kudin lita a gidajen mai inda mutanen gari su ke zuwa su saye man fetur din.

PMMC ta ce ta cire hannunta a farashin man babbar mota, ta bar ‘yan kasuwa su yi masa kudi. A halin yanzu dai darajar gangar danyen mai ya karye a duk wasu kasuwannin Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel