Ba a fara hangen karshen cutar COVID-19 a Najeriya ba tukuna – Shugaban PTF

Ba a fara hangen karshen cutar COVID-19 a Najeriya ba tukuna – Shugaban PTF

Gwamnatin tarayya ta sake jaddada cewa har yanzu akwai sauran aiki kafin a kai ga karshen annobar COVID-19 wanda ta hana Najeriya da sauran wasu kasashen Duniya sakat.

Jagoran kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar COVID-19 a Najeriya, Dr. Sani Aliyu shi ne ya bayyana haka a lokacin da kwamitin ya gana da manema labarai.

Dr. Sani Aliyu ya nuna cewa dole a tashi tsaye wajen yaki da wannan muguwar cuta da yanzu ta kashe fiye da mutane 100 a Najeriya. Aliyu ya ce wuka da nama su na hannun al’umma.

Jagoran kwamitin ya bayyana cewa cigaba da yaduwa da barkewar wannan cuta ya danganta ne da yadda mutane su ke bin doka a yayin da aka sassauta takunkumin kullen da aka maka.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Aliyu ya na cewa: “Dole mu yi duk abin da za mu iya na hana tashin alkaluma da sabuwar barkewar cutar a lokacin da aka sassauta takunkumin zaman gida.”

KU KARANTA: Adadin masu dauke da COVID-19 sun karu da mutum 195 a Najeriya

PTF ya yi kira ga gwamnoni musamman wadanda ba su kai ga tanadan dakunan da za a killace wadanda su ka kamu da cutar COVID ba, da su samar da daki mai cin gadaje akalla 300.

Ya ce: “Idan aka zo maganar dakunan killace masu dauke da cutar, an fi damuwa da wadanda ba su nuna wata shaida ko kananan alamun cutar, sahun irin wadannan ba a kai su asibiti.”

Idan ba ku manta ba kun ji cewa mafi yawan wadanda su ke dauke da cutar COVID-19 ba su bukatar a kwanatar da su a asibiti ko su yi amfani da na’urar da ta ke agazawa numfashi.

Shugaban hukumar NCDC, Chikwe Ihekweazu ya yi jawabi a wajen zantawar, ya ce su na amfani da wata na’ura da aka kirkira a lokacin annobar Ebola ne domin yakar Coronavirus a yau.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng