'Babu dadi, amma ya zama dole' - Zulum ya tsawaita wa'adin kulle jihar Borno

'Babu dadi, amma ya zama dole' - Zulum ya tsawaita wa'adin kulle jihar Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umar Zulum, ya roki jama'a su yi hakuri da yanayin da ake ciki yayin da ya ke sanar da kara tsawaita wa'adin kulle jihar Borno.

Da yammacin ranar Laraba ne gwamnatin jihar Borno ta mako guda a kan wa'adin rufe jihar sakamakon bullar annobar covid-19.

A cikin jawabin gwamna Zulum ga jama'ar jihar Borno, ya bayyana cewa kara tsawaita wa'adin rufe jihar ba zai yi wa jama'a dadi ba, a saboda haka ya bukaci su yi hakuri, yin hakan ya zama dole ne.

"Mun yi rashin manya da muhimman mutane a jihar Borno a cikin sati hudu da su ka gabata.

"Mun yi rashin shugabanni, dattijai, masana da 'yan kishin kasa. Mun yi rashin sarkin Bama, Shehu Kyari, tsohon gwamna, Alhaji Mohammed Goni, Galadima Modu Sheriff, Honarabul Wakil Bukar Lawan, Goni Modu Kolo, Goni Habib da wasu da dama.

"Na san babu dadi a ce an rufe jiha yayin da ake fama da zafin rana, ga shi mafi yawan jama'a su na azumin watan Ramadana.

"Bayan haka, mafi akasarin mutanenmu manoma ne, sai kananan 'yan kasuwa da ma su kananan sana'o'i da su ka dogara da kudin shiga da su ke samu a duk ranar da su ka fita harkokinsu na neman rufawa iyali asiri.

"Dokar kulle ta saka jama'a cikin wahala, rayuwa ta kara kunci a karkashin dokar hana zirga - zirga da rufe duk wasu harkoki na gwamnati da ma su zaman kansu.

'Babu dadi, amma ya zama dole' - Zulum ya tsawaita wa'adin kulle jihar Borno
Zulum da sabon Shehun Bama
Asali: UGC

"Zai fi kyautuwa mu sassauta dokar, to amma har yanzu ba samu magani ko rigakafin wannan cuta ba, ga shi kulllum adadin ma su kamuwa da kwayar cutar sai karuwa ya ke yi.

"Ba mu da wani zabi da ya wuce mu kara tsawaita dokar kulle tare da jaddada dokar nesanta domin takaita yaduwar kwayar cutar.

"Wannan annoba gaskiya ce, a saboda haka ya zamar ma na wajibi mu tashi tsaye mu yaketa," a cewar gwamna Zulum.

DUBA WANNAN: Karin wasu ma'aikatan lafiya 14 sun sake kamuwa da cutar korona a Kano

Gwamnan ya ce ya bayar da umarnin bude kasuwanni a ranar Alhamis, 7 ga wata, da Juma'a, 8 ga wata da kuma ranar Litinin, 11 ga wata.

Ya ce za a bude kasuwannin ne daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 5:00 na yamma domin bawa jama'a damar yin sayayya, kananan 'yan kasuwa kuma su samu kudin shiga.

Zulum ya shawarci jama'a su kasance ma su biyayya da duk matakan kare kai da dakile yaduwar annobar covid-19 yayin da su ka fita kasuwanni.

Ya umarci kwamitin kar ta kwana a kan yaki da cutar covid a kan ya dauki tsauraran matakai a kan matafiya daga wasu jihohi da ma su yin bulaguro da daddare domin tabbatar da ba a samu cigaba da yaduwar cutar a Borno ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel