Wasu masu cutar korona biyu sun tsere daga asibiti

Wasu masu cutar korona biyu sun tsere daga asibiti

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce mutum biyu da ke dauke da cutar korona a jihar ne suka yi layar zana.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, a wasu jerin rubutu da aka wallafa a shafin twitter, gwamnan ya ce akwai yuwuwar gida suka gudu.

Ya ce a halin yanzu jihar na fama da mutum 31 da ke dauke da cutar amma wasu daga cikin su bakin haure ne.

"Mun samu karin sakamakon gwajin wasu. Sakamako daya na ranar 3 ga watan Mayu na nuna mutumin na dauke da kwayar cutar. Mazaunin Ibadan ne," Makinde yace.

"Sakamakon mutum biyar da suka kamu da cutar na ranar 4 ga watan mayu ya kammala. Hudu daga cikinsu 'yan gudun hijira ne amma daya daga ciki mazaunin Oyo ne.

Wasu masu cutar korona biyu sun tsere daga asibiti

Wasu masu cutar korona biyu sun tsere daga asibiti
Source: UGC

"Sakamakon gwajin ranar 5 ga watan Mayu ya bayyana kuma an sake samun karin mutum biyar da ke dauke da cutar. Matafiya ne daga Arewacin Najeriya.

"Daga cikin mutum 33, biyu sun tsere kuma akwai yuwuwar mazauna garin nan ne.

"Mutum 10 sun killace kansu yayin da 21 suke cibiyar killacewa ta jihar Oyo.

"An kai samfur 975 kuma ana kokarin gwajinsu. Za ku iya kiran lambobin waya na gaggawa idan kuka ci karo da matafiya daga wasu jihohi."

A halin yanzu, jihar Oyo na da mutum 44 da suka kamu da cutar amma wasu daga ciki sun warke har an sallamesu.

KU KARANTA KUMA: Jami'in tsaro sun kama matafiya da almajirai 150 a Kaduna

A gefe guda, mun ji cewa karin wasu ma'aikatan lafiya 14 sun sake kamuwa da annobar cutar covid-19 a jihar Kano.

Da ya ke tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channel a ranar Laraba, shugaban kungiiyar ma'aikatan lafiya ta jihar Kano, Murtala Isa Umar, ya ce wadannan ma'aikatan ba sa cikin 32 da aka tabbatar sun kamu da cutar a ranar Talata.

Isah ya bayyana cewa ma'aikatan sun samu kwayar cutar ne yayin da su ke kula da marasa lafiya a asibitoci daban - daban da ke jihar Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel