Buhari ya bawa tsohon IGP Suleiman Abba babban mukami

Buhari ya bawa tsohon IGP Suleiman Abba babban mukami

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin tsohon shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Suleiman Abba, CFR, Mni, a matsayin shugaban amintattun da za su kula da asusun kudin lamuni na rundunar 'yan sanda.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya fitar a shafinsa na tuwita a ranar Laraba.

A cikin sanarwar, Garba Shehu ya ce dokar asusun kudin lamuni na rundunar 'yan sanda da aka kirkira a shekarar 2019 ta bawa shugaba Buhari ikon nada shugaba da mambobin da za su kula da asusun.

A cewar sanarwar, shugaba Buhari ya amince da nadin sakatare da mambobin asusun kudin lamunin kamar haka;

1. Ahmed Aliyu Sokoto – Babban sakatare

2. Mr Nnamdi Maurice Mbaeri – Wakilin ma'aikatar harkokin 'yan sanda

3. IGP Mohammed Adamu – Wakilin rundunar 'yan sanda

4. Usman Bilkisu – Mai wakiltar ma'aikatar shari'a

5. Mr Ben Akabueze (babban darektan kasafi da tsare - tsare na kasa) – Wakilin ma'aiktar kudi, kasafi da tsare - tsare

6. Engr. Mansur Ahmed – Wakilin kungiyar kwadago

7. Dr. Michael Bamidele Adebiyi – Wakilin kungiyoyi ma su zaman kansu

Garba Shehu ya ce nadin mutanen na daga cikin kokarin gwamnatin shugaba Buhari na kawo sauyi mai amfani a yadda ake gudanar da aikin dan sanda tare da samar da isassun kudi ga rundunar 'yan sanda.

Buhari ya bawa tsohon IGP Suleiman Abba babban mukami

Tsohon IGP Suleiman Abba
Source: Twitter

A watan Agusta na shekarar 2019 ne shugaba Buhari ya kirkiri asusun lamunin yayin sake fasalin ma'aikatar kula da 'yan sanda.

"Shugaban kasa ya yabawa gwamnoni, mambobin majalisar kasa da sauran 'yan Najeriya bisa kishinsu da kokarinsu na ganin an kawo gyara a fasalin aikin dan sanda domin tabbatar da tsaro a cikin kasa," a cewar Garba Shehu.

DUBA WANNAN: Ganduje ya nada Kabiru Inuwa a matsayin sabon sarkin masarautar Rano

Ministan harkokin 'yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi, zai sanar da ranar da za a rantsar da Abba da sakatarensa da sauran mambobin da shugaba Buhari ya nada.

Suleiman Abba, dan asalin jihar Jigawa, ya tsaya takarar neman kujerar sanata a zaben shekarar 2019.

Sai dai, takararsa ta gamu da babban cikas bayan uwar jam'iyyar APC ta kasa ta ki tantance shi duk da ya sayi fom din takara bisa ka'ida.

Jam'iyyar APC ba ta bayar da wani dalili na yin watsi da takarar Abba ba duk da kasancewarsa mamba a cikinta.

Jin haushin hana shi takara ya sa Abba ya ziyarci ofishin uwar jam'iyyar APC a Abuja tare da yin tsinuwa ga duk mai hannu a hana shi yin takarar a mazabarsa ta Jigawa ta tsakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel