Yanzu-yanzu: Jirgin da ya kwaso 'yan Najeriya daga Dubai ya yi juyawar gaggawa

Yanzu-yanzu: Jirgin da ya kwaso 'yan Najeriya daga Dubai ya yi juyawar gaggawa

Wata mata 'yar Najeriya ta haihu a jirgin sama yayin da ake kwaso su daga UAE, jaridar The Punch ta wallafa.

Shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya da ke kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa ta tabbatar da aukuwar lamarin a yau Laraba.

Amma kuma bata bayyana me aka samu ba duk da ta ce uwar da jaririn suna lafiya.

Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya ce 'yan Najeriya 265 ne za su isa jihar Legas daga Dubai a ranar Laraba.

Yanzu-yanzu: Jirgin da ya kwaso 'yan Najeriya daga Dubai ya yi juyawar gaggawa
Yanzu-yanzu: Jirgin da ya kwaso 'yan Najeriya daga Dubai ya yi juyawar gaggawa
Asali: UGC

Hakan yana daga cikin kokarin gwamnatin Najeriya na dawo da 'yan kasarta gida a yayin da ake tsaka da annobar korona.

"A yayin dawo da 'yan Najeriya gida daga kasashen ketare, ma'aikatar harkokin waje tare da NCDC za su killace wadanda suka iso.

"Jirgin kamfanin Emirates zai kawo kashi na farko na 'yan Najeriya 265 daga Dubai. Za su sauka da karfe 3 na yamma a filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Ikeja a Legas," Onyeama yace a wata takarda da ta fito daga kakakinsa.

Amma wata majiya mai kusanci da kamfanin jirgin saman ta ce sai karfe 10 na safe jirgin ya tafi Dubai kuma dukkan fasinjojin an tabbatar basu dauke da cutar.

Kamar yadda majiyar tace, wata mata ta haihu bayan sa'a daya da fara tafiya kuma dole ta sa matukan jirgin suka juya don ajiye mahaifiyar da jaririn.

KU KARANTA KUMA: Baku isa ku fadawa Buhari abinda zai yi ba - Mai magana da yawunsa

An yi kokarin samun ministan ta wayar tafi-da-gidanka amma hakan ya gagara.

Shugaban NIDCOM ta tabbatar da lamarin ta hanyar sakon kar ta kwana da ta tura mai cewa, "Tabbas jirgin ya juya. Mahaifiyar da dan duk suna lafiya."

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na fara kwaso 'yan Najeriya da suka kasa dawo gida a wasu kasashen ketare sakamakon hana zirga-zirga da annobar korona ta janyo.

Ma'aikatar kasashen wajen Najeriya, ita ta sanar da hakan a kan shafinta na Twitter a ranar Talata, 5 ga watan Mayun 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng