Mutane 156 sun mutu a cikin kwana 6 a Yobe

Mutane 156 sun mutu a cikin kwana 6 a Yobe

- Annobar yawaitar mace - mace na cigaba da kara karfi a jihohin arewacin Najeriya

- Yawaitar mace - macen ta fi shafar tsofin mutane da ke fama da wasu cututtuka da su ka hada da hawan jini, ciwon sukari, ciwon koda da sauransu

- Mace - macen jama'a, wacce ke kama da irinta jihar Kano, ta jefa tsoro da zaman zulumi a tsakanin mazauna kananan hukumomin Gashua da Potiskum a jihar Yobe

A kalla mutum 155 ne su ka mutu a cikin kwanaki 6 a kananan hukumomin Gashua da Potiskum da ke jihar Yobe.

A cewar jaridar SaharaReportes, mutanen na nuna alamu da ke kama da na ma su dauke da kwayar cutar covid-19 kafin su mutu.

Yawaitar mace - macen, wacce ke kama da irinta jihar Kano, ta jefa tsoro da zaman zulumi a tsakanin mazauna kananan hukumomin.

Wani kwamitin bincike da shugaban kasa ya tura Kano ya alakanta yawaitar mutuwar mutanen jihar da annobar covid-19.

Wata majiya ta sanar da SaharaReporters cewa a kalla mutane 98 ne su ka mutu a karamar hukumar Potiskum a tsakanin ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, zuwa ranar Talata, 5 a watan Mayu.

Mutane 156 sun mutu a cikin kwana 6 a Yobe

Gwamnan Yobe; Mai Mala Buni
Source: Twitter

"Babu wurin da ya kai makabartu cikar jama'a a garuruwan biyu.

"A kalla mutane 57, yawancinsu dattijai, sun mutu a garin Gashua. Amma duk da haka kwamitin kar ta kwana a kan covid-19 bai farka daga baccin da ya ke yi ba a Damaturu," a cewar wata majiyar SaharaReporters.

DUBA WANNAN: A karshe, ministan lafiya ya bayyana magananin da FG ta amince da amfani da shi a kan ma su jinyar covid-19

SaharaReporters ta yi zargin cewa gwamnan jihar Yobe ya tare a Abuja tun bayan zabensa, kuma har yanzu bai koma jiharsa ba domin fuskantar kalubalen da ya sako jama'a a gaba ba.

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya bawa sarakunan jihar 14 kyautar motocin alfarma da kudinsu ya kai miliyan N600 duk da talaucin da jama'ar jihar ke fama da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel