An yankewa wani mutum hukuncin bulala 5 a kan laifin take dokar kulle a Kano

An yankewa wani mutum hukuncin bulala 5 a kan laifin take dokar kulle a Kano

- Wata kotun tafi-da-gidanka a jihar Kano ta yankewa wani mutum mai matsakaicin shekaru hukuncin bulala biyar

- Hakan ya biyo bayan take dokar takaita zirga-zirga a jihar da ya yi

- Kotun ta yankewa mutum 14 hukunci sakamakon kama su da tayi da laifin kaiwa da kawowa ba tare da wani dalili ba

Wata kotun tafi-da-gidanka a jihar Kano ta yankewa wani mutum mai matsakaicin shekaru hukuncin bulala biyar a kan laifin take dokar takaita zirga-zirga a jihar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, kotun mai zama a karamar Gwale wacce alkali Salisu Idris ke jagoranta, ta kama mutumin da laifin take dokar tare da yanke masa hukunci.

Amma kuma, wanda ake yankewa hukuncin ya karba hukuncinsa a take.

An yankewa wani mutum hukuncin bulala 5 a kan laifin take dokar kulle a Kano
An yankewa wani mutum hukuncin bulala 5 a kan laifin take dokar kulle a Kano
Asali: Twitter

Kotun ta yankewa mutum 14 hukunci sakamakon kama su da tayi da laifin kaiwa da kawowa ba tare da wani dalili ba.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Abinda ke mayar mana da aiki baya a Kano - Boss Mustapha

An yankewa wadanda aka kama hukuncin fansar kansu tare da ayyuka ga yankin da suke a matsayin hanyar hukunta su.

A gefe guda, an sallami mutum uku da ke jinyar cutar covid-19 bayan sun warke a jihar Kano, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta jihar ta sanar a ranar Laraba.

Wanan shine karo na farko da aka samu labarin warkewar wani mai dauke da kwayar cutar coronavirus a jihar Kano.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiya a Kano ta fitar ranar Laraba a shafinta na tuwita.

Ya zuwa yanzu adadin ma su dauke da cutar coronavirus ya kai mutum 397, a cewar ma'aikatar.

A cewar ma'aikatar, an samu karin sabbin mutane 32 da annobar ta harba ranar Talata a jihar Kano.

Zuwa ranar yau Laraba, 6 ga watan Mayu, a kalla mutum miliyan 3.6 suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya. An samu warakar mutum 1.2 amma an rasa rayuka 252,000 a fadin duniya.

Tun bayan bullowar cutar a Najeriya, mutum 2,950 ne suka kamu da cutar yayin da mutum 481 ne suka warke daga jinyar cutar. Mutum 98 ne suka rasa rayukansu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel